Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nada Malam Salihu S. Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna da nufin ganin an samu nasarar gudanar da ayyukan Hajji na 2024.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Mohammed Lawal Shehu ya fitar ta ce, sakataren kwamitin na musamman kan aikin hajjin 2024 zai yi aiki a matsayin sakataren gudanarwa na hukumar.
- Harin Bam A Kaduna: Sanatoci 109 Sun Bayar Da Gudummawar Albashinsu Naira Miliyan 109
- Mali Da Nijar Za Su Kawo Karshen Yarjejeniyar Haraji Da Faransa
Ta Kara da cewa, sauran mambobin kwamitin, za su gudanar da ayyukansu tamkar mambobin gudanarwar hukumar jin dadin Alhazan.
Sanarwar ta ce, an mayar da Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu zuwa Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Kaduna (KEPA) a matsayin Manajan Darakta.