Gwamnatin Jihar Kano ta amince ta biya diyyar Naira biliyan uku ga kungiyar masu shagunan Masallacin Idi saboda rusa musu kadarorin da aka yi musu ba bisa ka’ida ba.
An cimma yarjejeniyar ne ta wata takardar neman sasanci a ranar 12 ga watan Disamba tare da gabatar da kara a ranar 13 ga watan Disamba ta hannun lauyoyi ga masu shari’a, Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
- Yadda Matashi Ya Yi Yunƙurin Hallaka Matarsa Don Ya Samu Damar Sace Mata Talabijin
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 13, Sun Ceto Mutane 268 A Katsina
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayyana hakan ne biyo bayan rushe shagunan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Masu shagunan sun kai karar gwamnatin jihar da hukumar tsare-tsare ta Jihar Kano (KNUPDA); babban lauyan gwamnati, ‘yansanda; Mataimakin Sufeto Janar na ‘yansanda shiyya 1 da ke Kano; Kwamishinan ‘yansanda, Kano; Kwamandan Hukumar Tsaro da Tsaron Farar Hula (NSCDC) kara.
Mai shari’a Samuel Amobeda, a ranar 29 ga watan Satumba a wani hukunci da ya yanke, ya umuaci gwamnatin jihar ta biya ‘yan kasuwar naira biliyan 30 a matsayin diyyar Naira biliyan 250 da ‘yan kasuwar ke nema, kan rushe musu kadarorin da aka yi.
Amma sakamakon kin bin umarnin kotun Kano da gwamnatin jihar ta yi, ‘yan kasuwar sun shigar da karar a gaban mai shari’a Ekwo, inda suka nemi a tilasta wa gwamnatin biyan su.
Hakan ne ya sa kotu bada umarnin rufe asusun ajiyar bankin gwamnatin jihar kan kin bin umarninta.
Sai dai kuma da aka ci gaba da sauraren karar a ranar Alhamis, Lauyan masu kara, Dokta N. A. Ayagi, ya shaida wa kotun cewa bangarorin biyu sun cimma matsayar biyan kudin.
Daga nan sai Ayagi ya bukaci kotun da ta amince da shirin sansancin cikin masalaha.
Har ila yau, lauyan wadanda ake kara, Affis Matanmi, bai ce komai kan hakan ba, don haka mai shari’a Ekwo ya yanke hukuncin kamar yadda bangarorin biyu suka aminta.