Daya daga cikin fasihan marubutan littafin hausa na yanar gizo MUGIRAT MUSA FANA, ta bayyana wa masu karatu abin da ya ja hankakinta har ta tsunduma cikin rubutu, ta kuma bayyana irin burukan da ta kudurce game da rubutu, ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:
Ya sunan hazikar?
Sunana Mugira Musa Fana
Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinki.
Ni haifafiyar garin Kebbi ce, ina zaune a garin birnin kebbi, acikin garin birnin kebbi nayi karatuna tun daga firamare, sakandare, har zuwa jami’a, a taikace dai ni ‘yar Jihar kebbi ce kuma marubuciya.
Me ya ja hankakinki har ki ka fara rubutu?
A taikace tun ina makarantar firamare nake karatun littafi, kuma har cikin zuciyata ina kaunar marubuta da sha’awar kasancewa daya daga cikinsu, kwatsam wata rana sai ubangiji ya hadani da wasu marubuta, na bayyana musu kudurina suka jajirce wurin bani goyon baya don ganin na cimma burina na zamowa marubuciya, Alal hakika marubuta suna da hadin kai tare da kaunar ci gaban junansu.
Kamar wanne bangare ki ka fi maida hankali a kai wajen rubutu?
Soyayya, Tausayi, Cin Amanah.
A cikin littattafan da ki ka rubuta ko akwai wadanda ki ka buga?
Gaskiya ba wanda na buga, amma ina sa ran bugawa nan gaba idan Ubangiji ya yarda kuma ya bani tsawon rai.
Wanne irin kalubale ki ka fuskanta game da fara rubutu?
Maganar gaskiya ban fuskanci wani kalubale a game da rubutana daga wurin iyaye, ‘yan uwa ko abokai ba, sun bani goyon baya tare da jin dadin kasancewata marubuciya. Saboda ko a cikin unguwarmu aka yi baki za su ganin wace ce marubuciya Mugirat Musa Fana, kuma ko a kauyenmu Fana suna matukar alfaharina da ni tare da nuna min kauna ta musamman.
Wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alhamdulilahi ala kullin halin na samu nasarori da dama a rayuwata a sanadiyyar rubutu, saboda a yanzu da ka fadi sunana Mugirat Musa an sanni, kuma na san wasu a dalilin rubutu ana mutunci, na samu alkairori da dama a sanadiyyar rubutu.
Toh ya batun masu karanta littattafanki ko abokan rubutunki, shin kin taba fuskantar kalubale daga gare su ko kuwa?
A’a ban taba fuskantar kalubale ga masu karatu ba, illa kalubale daya shi ne rashin Sharhi.
Kamar da wanne lokaci ki ka fi jin dadin rubutu?
Ina jin dadin rubutu da safe da kuma dare, sune lokuttan yin rubutuna.
Wanne abu ne ya taba bata miki rai game da rubutu?
Maganar gaskiya babu wanda ya taba batamin rai game da rubutu, saboda ni abin da yake gabana kawai shi ne danuwata.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Rubutu baiwa ce kuma abu ne mai matukar muhimmanci da daraja, wanda ba kowa bane Ubangiji ya bashi wannan baiwar.
Mene ne burinki game da rubutu?
Babban burina game da rubutu shi ne na zamo sananniyar marubuciya wanda kasar Nijeriya za ta yi alfahari da ita.
Bayan rubutu kina yin wata sana’ar ne?
Ina taba sana’ar sayar da Takalman roba.
Ya ki ke iya hada sana’arki da kuma rubutunki?
Ko wane akwai lokacin yinsa, sana’a da kuma Rubutu.
Shin kina da aure ko babu?
A’a ba ni da aure, amma na kusa, kwanan watan aurena 13/01/2024 da yardar Allah.
Me za ki ce da masu karanta littattafanki?
Ina yi wa dukkan makatanta littafaina fatan Alkhairi, ubangiji ya saka musu da mafificin alkhairi ya bar zumunci.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaida yayuna abin alfaharina; Anti Raheenat M Abubakar, Anti Hadiza D Auta, Antu Naja’atu Ibrahim, Fiddausi Sani, da kuma Maman Afrah.