Tsohon shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya danganta ziyarar da wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki suka kai wa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin bata lokaci.
Gwamnonin sun kai ziyarar ne a garin Fatakwal a jiya juma’a gwamnonin su ne, na jihohin Lagos Babajide Sanwo-Olu, da na Ekiti Kayode Fayemi da kuma na Ondo Olurotimi Akeredolu.
- Babu Aibu A Zabar Musulmi 2 A Matsayin ‘Yan Takara – Ladoja
- Baragurbi Ke Bata Ayyukan Kare Hakkin Yara – Hajiya Aisha
Saraki ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a garin Ilorin da ke jihar Kwara jim kadan bayan tashi daga sallar Idi, inda ya kara da cewa, ziyarar a karshe ba za ta haifar da komai ba domin PDP ba za ta yarda Wike ya koma APC ba.
Ya bayyanan cewa, Wike mutum ne mai mahimmancin gaske ga PDP, inda ya sanar da cewa, nan ba dadewa ba PDP za ta warware dukkan matsalolinta na cikin gida.