Tsoho Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya ce ya yanke shawarar janyewa daga lamuran siyasa saboda ya fuskanci yana samun damuwa da lamuran siyasa babu gaira babu dalili.
BBC ta ce, Sanata Adamu ya bayyana haka ne a ranar Asabar a garin Lafiya yayin wani bikin ƙaddamar da wani littafi da aka yi wa take da “Gwamnati mai ci gaba: nuna nasarorin da Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya samau daga 2019 zuwa 2023,” wanda Abdullahi Tanimu ya rubuta.
- Ƙasa Da Sa’o’i 24 Da Sauka: EFCC Ta Ziyarci Tsohon Shugaban APC Abdullahi Adamu
- Abdullahi Adamu Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa
Da yake tsokaci kan littafin Abdullahi Adamu ya yaba wa marubucin tare da shawartar ‘yan jihar su ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa.
Ya ce “Ba wai ritaya kawai na yi ba, na janye hannuna daga lamuran siyasa. na ci ina samun matsala da siyasa da lamuranta a ‘yan kwanakin nan.
“Ku gafarce ni, ba zan iya ƙara cewa komai ba dangane da siyasa bayan neman haɗin kai da zan so ku ci gaba da baiwa gwamnati.
“Yana buƙatar duk taimakonku da addu’o’inku domin nasararsa,” in ji Adamu.