Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargin barayin shanu ne tare tare da nasarar kwato dabbobi 90 a ranar Asabar a Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Nijeriya ranar Lahadi a Kaduna.
- Harin Bam A Kaduna: Sanatoci 109 Sun Bayar Da Gudummawar Albashinsu Naira Miliyan 109
- Kaduna: Muna Neman Afuwar Kisan Masu Maulidi – Hafsan Sojin Kasa
Hassan ya ce, “A ranar 16 ga watan Disamba, da misalin karfe 21:30, jami’an mu da ke sintiri a kusa da Kasuwar Dole a cikin Millennium, sun yi nasarar cafke wanda ake zargin.
“Wanda ake zargin dan yankin Kurmi ne a karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.”
Hassan ya bayyana cewa wanda ake zargin yana da hannu a cikin satar shanu 65 da tumaki 25.
Ya ce bayan bincike da kuma yi masa tambayoyi, wanda ake zargin bai iya bayar da gamsasshen bayani kan dabbobin ba.
“Hakan ya haifar da shakku game da sa hannunsa a zagin satar.
“Sakamakon hakan, an mika wanda ake zargin ga hukumar binciken manyan laifuka (CID). don yin cikakken bincike,” inji Hassan.
Ya kara da cewa yankin ya samu kwanciyar hankali yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyuka kai samame, jami’an ‘yan sandan gani da ido daga ‘yan sintirin yankin don tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.