Jam’iyyar APC ta bayyana aniyarta na garzayawa Kotun Koli, da nufin kwato abin da ta kira hakkinta a hannun gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.
Shugaban jam’iyyar, Barista Idris Sha’aibu, ya ce, “wannan hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, a matsayin zababben Gwamna Jihar Adamawa bai yi mana dadi ba.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Fintiri A Adamawa
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa
“Jam’iyya za ta saurari duk masu ruwa da tsaki domin daukaka kara a mataki na gaba, dole za mu kalubalanci wannan hukuncin kotun.
“Kamar yadda muka Fara za mu kai har karshe, kuma babu sauran hutu har sai munga karshen tafiyar kamar yadda muka ga farkonsa” Cewar Idris.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp