• English
  • Business News
Wednesday, July 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kama Ma’auratan Da Suka Sayi Jaririn Wata 1 A Kan 30,000

by Sadiq
2 years ago
in Labarai
0
Kirsimeti: An Tsaurara Tsaro A Kwara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta yi nasarar cafke wasu ma’aurata da ke da hannu wajen safarar wani jariri dan wata daya.

Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun sayi jaririn ne a hannun mahaifiyarsa da ke unguwar Ajah a jihar Legas kan kudi kadan kan kudi naira 30,000.

  • An Ceto Mutumin Da Ya Shafe Wata 6 A Hannun ‘Yan Bindiga A Kaduna
  • NLC Ta Ki Amincewa Da Umarnin Hana Ma’aikata Saka Dogayen Kaya A Neja

Har yanzu dai ba a bayyana sunayen ma’auratan ba, amma jami’an ‘yansanda sun cafke su a Onitsha  lokacin da suke kokarin shiga wata mota da jaririn a ranar Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya bayyana cewa ‘yansandan sun yi gaggawar ceto jaririn tare da mika shi ga ma’aikatar harkokin mata da kananan yara ta jihar.

Tochukwu ya ci gaba da cewa, an mika ma’auratan ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) ta jihar domin ci gaba da bincike.

Labarai Masu Nasaba

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

A cewarsa an gano su a lokacin da wani fasinja da ke cikin motar  ya sanar da ‘yansanda yana  zargin cewa ma’auratan na dauke da jaririn da ba nasu ba.

Ya bayyana cewa mai ba da labarin ya sanar da ‘yansanda cewa ya lura cewa a lokacin da suke tafiya daga Legas, jaririn na kuka, amma matar ta gaza ba shi nono.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aderemi Adeoye, ya yaba wa mutumin kan taimaka wajen ceto yaron.

Ya kuma yaba da kwazo da taka-tsan-tsan da jami’an ‘yansanda suka yi wajen magance lamarin cikin gaggawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yan SandaAnambraJaririLegasMa'aurata
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Ceto Mutumin Da Ya Shafe Wata 6 A Hannun ‘Yan Bindiga A Kaduna

Next Post

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Tambuwal Da Wamakko A Matsayin Sanatoci

Related

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang
Manyan Labarai

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

2 hours ago
David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
Manyan Labarai

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

4 hours ago
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu
Labarai

Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato

5 hours ago
An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa
Labarai

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

14 hours ago
Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya
Labarai

Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

14 hours ago
Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma
Labarai

Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

15 hours ago
Next Post
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Tambuwal Da Wamakko A Matsayin Sanatoci

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Tambuwal Da Wamakko A Matsayin Sanatoci

LABARAI MASU NASABA

Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea

Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea

July 2, 2025
Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

July 2, 2025
David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

July 2, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu

Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato

July 2, 2025
An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

July 1, 2025
An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

July 1, 2025
Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

July 1, 2025
Kayan Aro Baya Rufe Katara

Kayan Aro Baya Rufe Katara

July 1, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

Askarawan Zamfara Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga, Kacalla Ɗanbokolo Ubangidan Turji

July 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.