Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC), a Jihar Neja ta nuna rashin amincewa da umarnin gwamnan jihar, Umar Muhammad Bago, na hana ma’aikata saka manyan kaya zuwa aiki daga ranar Litinin zuwa Alhamis.
Gwamnan ya bayar da wannan umurni ne a wani jawabin da ya gabatar a lokacin kaddamar da wani aikin noman Shikafa a jihar a ranar Lahadi.
- Kotu Ta Haramta Wa Tsohuwar Minista Rike Mukami A Nijeriya
- Nijar Ta Cika Shekaru 65 Da Samun ‘Yancin Kai
Kungiyar Kwadago ta ce umarnin da gwamnan ya bayar ba shi da wani tasiri, domin duk wani tsari na aikin gwamnati a jihar yana karkashin doka, kamar yadda shugaban kungiyar a Jihar Neja, Kwamred Abdulkarim Lafane ya fada.
Tuni dai masana kundin tsarin mulkin Nijeriya suka fara sharhi kan wannan sabon batu.
A yanzu dai kallo ya koma a tsakanin ma’aikatan Jihar Neja da kuma gwamnatin jihar domin ganin yadda wannan tirka-tirka za ta kaya.
Kazalika kalaman na gwamnan jihar ya yamutsa hazo.