‘Yan bindiga sun kai hari Karamar Hukumar Yoro a Jihar Taraba, inda suka yi garkuwa da wata mata mai juna biyu, ‘yan lsanda biyu, da wasu mutane 21.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana cewa maharan dauke da makamai sun afkawa al’ummar Pupule da sanyin safiyar Talata, dauke da muggan makamai.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Tambuwal Da Wamakko A Matsayin Sanatoci
- NLC Ta Ki Amincewa Da Umarnin Hana Ma’aikata Saka Dogayen Kaya A Neja
Maharan sun ta bude wuta ba kakkautawa, lamarin da ya sanya tsoro a zukatan mazauna yankin sannan suka yi awon gaba da wasu.
A cewar Mista Tundu Ibahem, daya daga cikin mutanen kauyen, ya ce an sace hakimin mai daraja ta biyu na yankin, Alhaji Umaru Abubakar tare da dansa.
‘Yan bindigar sun kuma sace wata mata mai juna biyu da wasu ‘yan uwanta da dama.
“Mutanen Pupule na nan a kan gadaje, ‘yan bindigar sun mamaye yankin a kan babura, sun haura sama da gida 20 kuma suna dauke da muggan makamai, sai harbe-harbe suke,” in ji Ibahem.
Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda biyu; sufeto da sajan— na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, tare da wasu mutane 16 daga yankin Pupule.
Usman ya tabbatar da cewa rundunar ta aike da jami’an ‘yansanda zuwa yankin.