Hukumar Karfafa Zuba Jari A Nijeriya (NIPC) ta bayyana cewa, ta kammala tattauanwa da wasu kamfanonin kasa Jamus 22 don shirin yadda za su zuba jarin fam Biliyan 3 a bangarori daban daban na tattalin arzikin kasar nan.
Shugabar hukumar, Misis Aisha Rimi ta sanar da haka a Abuja, ta kuma kara da cewa, kamfanonin 22 na kasar Jamus sun nuna sha’awar su na zuba jari a bangarori da dama na tattalin arzkin Nijeriya.
A jawabinsa, ministan harkokin kasashen waje, Yusuf M. Tuggar ya ce, “Tattaunawa tare da hadin kai a tsakanin Nijeriya da kasashen Turai ya nuna cewa, 3 daga cikin 5 na kasashen da Nijeriya ke fitar da kayayyakin su suna Turai ne, wannan kuma kididdiga ne na zango na 4 na shekarar 2022. Ya kara da cewa, adadin kasuwancin da Nijeriya ta gudanar a shekarar 2022 ya kai na Yuro Biliyan 3 kuma Nijeriya ta fitar da kayayyaki har na Dala Miliyan 806 33 a daidai wanann lokacin.”
Shugabar Hukumar, Aisha Rimi ta lura da cewa, suna gudanar da taruka a kai kai tare da jihohi don sanin halin da suke ciki, ta haka masu zuba jari za su amfana tare da sanin wuraren da ya kamata su zuba jarinsu.
Haka kuma shugaban tawagar kasar Jamus a taron, Micheal Schmidt ya ce, kamfanonin su 22 sun zagaya jihohin Nijeriya daban-daban sun kuma aminta da zuba jari a jihohi daban-daban a bangarori daban daban na tattalin arziki.