Hukumar kula da kwallon kafa ta Nijeriya (NNL) ta ci tarar kungiyar Mailantarki Care Naira Miliyan Daya saboda gazawa wajen shawo kan magoya bayanta a karawar da suka yi da Adamawa United a ranar Lahadin da ta gabata.
An rahoto cewa, magoya bayan Mailantarki Care sun yi ta batanci ga alkalan wasan a yayin karawar. Hakan kuma ya sabawa ka’idojin aiki na NNL.
- Muna da Yakinin ACF Za Ta Ci Gaba Da Kare Muradun Arewa – Matasan Arewa
- Tsarabar Kirsimeti: Yadda Wolves Ta Zazzaga Wa Chelsea Ci A Gasar Firimiya
Babban jami’in gudanarwa na NNL, Dr Ayo Abdulrahman ya gargadi kungiyar cewa, za’a saka mata takunkumi mai tsauri idan irin hakan ta sake faruwa.
An bukaci Mailantarki da ta biya tarar nan da ranar 6 ga watan Janairu na shekarar 2024.
Bayan haka, an dakatar da kocin Mailantarki Care, Sulaiman Usman; Sakataren kungiyar Adamu Usman; da Kodinetan kungiyar, Auwal Kamuwa na tsawon watanni biyu daga shiga duk wasu harkokin NNL.