Kungiyar tuntuba ta “Katsina Consultative Forum” za ta shirya wani taron tattaunawa a kan matsalar shaye-shaye da suke yi wa zaman lafiya Jihar Katsina da Kasa barazana wanda kuma ake sa ran cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na daga cikin manyan baki da za su halarci wannan taro a Katsina.
Shugaban Kungiyar Tuntuba na Jihar Katsina, Alhaji Aliyu Abubakar Danmusa ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai wanda ya yi karin haske kan yadda taron zai kasance da kuma dalilin da ya sa suka sauki matsalar shaye-shaye a matsayin batun da za su tattauna a kansa.
- Gwamna Bago Ya Yi Watsi Da Rahoton Haramta Sayar Da Giya A Neja
- Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Kasuwannin Shanu 11 Saboda Matsalar ‘Yan Bindiga A Jihar
Ya kara da cewa an gayyato masana daga kowane bangare domin baje kolin hanyoyin da za a yi amfani da su domin sannin hanyar da za a tunkari wannan annoba ta sha da fataucin miyagun kwayoyi da suke haifar da abubuwa marasa kyau a cikin al’umma.
Haka kuma ya yi bayanin cewa ba harkar shan kwayoyi ba ce kadai matsala ba, yana mai cewa sannu a hankali za su rika daukar matsalolin daya bayan daya domin tattaunawa akan su tare da lalubu hanyoyin da gwamnatin da kuma masu ruwa da tsaki za su bada gudunmawa domin magance su.
“Mun lura cewa matsalar kwaya, ita ce ke jagoranci zuwa ga aikata manyan laifufuka da suka hada shiga harkar ‘yan bindiga da fashi da makami da fyade da sauran manyan laifufuka, saboda haka dole mu hada hannu domin tunkarar wannan matsala baki dayanmu” in ji shugaban.
Alhaji Aliyu Abubakar ya kara da cewa wannan taron zai samu tagomashi daga masana da masu ruwa da tsaki da za su baje kolin basirarsu a kan wannan matsala, mutane irin su Dakta Usman Bugaje masanin magunguna da siyasa da shugabar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta jihar Katsina, Dakta Asma’u Abdulkadir da kuma mai baiwa gwamnan Katsina shawara akan hana sha da fataucin kwayoyi na da cikin manyan baki a wajen taron
A cewarsa halartar manyan baki irin su tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda da Sarakunan Katsina da Daura na daga cikin abubuwan da za su karawa taron armashi da fatan cewa za a yi abainda ya kamata akan wannan matsala.
Haka kuma ya yi bayanin cewa an gayyaci matasa wadanda sune wannan matsala ta shafa kai tsaye musamman daliban jami’o’i da matasa masu yi wa kasa hidima da kungiyoyin da ba na gwamnati ba.
Wannan taro kamar yadda shugaban wannan kungiya ya bayyana za a gudunar da shi a ranar 31 ga watan Disamba, 2023 a baban dakin taron na masaukin shugaban kasa da ke fadar gwamnatin Jihar Katsina.