Wata budurwa mai shekaru 23, mai suna Amanda Uchechi Ugo, ta harbe jami’in dan sanda Cosmos Ugwu har lahira a ofishin ‘yansanda na Ezinihitte da ke Jihar Imo.
Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Talata, 26 ga watan Disamba, a ofishin ‘yansanda na Ezinihitte da ke Karamar Hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar.
- Yadda Aka Shirya Wa ACG James Sunday Bikin Taya Murnar Karin Girma A Gombe
- Buhari Zai Halarci Taron Tattaunawa Da Kungiyar Tuntuba Ta Katsina
Lamarin da ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yamma a ranar washegarin ranar Kirsimeti.
Da jin karar harbi uku daga ofishin dan sandan ragowar jami’an da ke aiki suka buya domin neman tsira.
“Lokacin da jami’an suka shiga ofishin, sai suka tarar da Kofur Ugwu a kwance babu rai cikin jini.”
Wata majiyar ‘yansanda a jihar ta ce, “Ta yi masa harbi uku; biyu a kirjinsa daya kuma a hannunsa na hagu.
“Marigayin da budurwar sun yi cece-kuce kafin faduwar lamarin.
“A yayin rikicin, budurwar ta yi amfani da bindigar Kofur Ugwu tare da harbe shi har lahira.”
Majiyar ta kara da cewa “Al’amarin ya kasance kamar a fim a ce wai an harbe dan sanda a ofishinsa.”
Sai dai ta zuwa yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan faruwar lamarin ba.