Mai magana da yawun kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC Xu Dong, ya bayyana rashin gamsuwa da rashin amincewa da kakkausar murya, kan munanan tanade-tanade dake da alaka da kasar Sin, a cikin dokar kasafin kudi ta shekarar 2024 mai nasaba da ba da iznin tsaron kasa ta Amurka, wacce kwanan nan aka sanyawa hannu.
Kakakin ya ce, kudirin da ke da alaka da wannan doka, yana magana ne kan batun yankin Taiwan, da ba da shawarar yin takara bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, da daukar Sin a matsayin barazana, da kuma yayata rage barazana a muhimman fannonin hulda da kasar Sin.
- Hadin Kan Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Zuba Jari Game Da Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ya Samu Ci Gaba Akai-Akai A Bana
- Kwamitin Kolin JKS Ya Gudanar Da Taron Tunawa Da Cika Shekaru 130 Da Haihuwar Mao Zedong
Ya bayyana cewa, hakan tamkar yin katsalandan ne ga harkokin cikin gidan kasar Sin matuka, da neman yin illa ga ‘yancin kai, da tsaro da ci gaban kasar Sin, kuma ya keta yarjejeniyar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma a taron San Francisco.
Kakakin ya ce, batun yankin Taiwan, ainihin tushen moriyar kasar Sin ne, kana ginshikin tushen siyasa a alakar kasashen Sin da Amurka, kuma jan layi na farko da ba za a ketare ba a dangantakar kasashen biyu.
Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin a ko yaushe tana bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, kana tanade-tanaden Amurka sun yi watsi da gaskiya, suna kuma ba da shawarar mayar da wata kasa saniyar ware, da siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, da fasaha da al’adu bisa son rai, da kokarin dakile mu’amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka.
Xu ya ce, mutunta juna, zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwar samun nasara tare, su ne alkiblar kokarin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka.
Sannan, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya bayyana a yau Alhamis cewa, rundunar sojin kasar Sin ta nuna matukar rashin gamsuwa da kuma adawa da amincewar da Amurka ta yi da sanya hannu kan dokar ba da izinin tsaron kasa na shekarar kasafin kudi na 2024, wanda ke kunshe da abubuwan da ba su dace ba da suka shafi kasar Sin.
Wu ya ce, wannan mataki da suka dauka ba tare da wata hujja ba akan abin da suke kira “barazanar sojin kasar Sin” katsalandan ne ga harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma yana yin illa sosai ga ‘yanci kai, da tsaro da ci gaban kasar Sin. (Ibrahim Yaya, Muhammed Yahaya)