A karkashin shirinsa na sake fasalta tsarin kiwon lafiya ( 2019- 2023), gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da daukan sabbin ma’aikatan kiwon lafiya 440 da za a tura sassa daban-daban na asibitocin da suke fadin jihar.
Wannan bayanin na kunshe ne ta cikin sanarwar da shugaban kwamitin daukan ma’aikatan lafiya Dakta James B. Madi ya sanya wa hannu tare da rabar wa ‘yan jarida a madadin babban sakataren hukumar kula da lafiya tun daga matakin farko ta jihar (SPHCDA), Dakta Abdulrahman Shuaibu.
A cewar sanarwar, matakin da gwamnan ya cimma na daukan ma’aikatan ya yi ne da zimmar kokarin shawo kan karancin ma’aikatan kiwon lafiya da ake fama da su tare da kokarin bunkasa kiwon lafiya a jihar musamman a kananan asibitoci.
Don haka, hukumar lafiya a matakin farko ta jihar da hadin guiwar Global Alliance for Vaccine and Immunization (GAVI) ke kiran wadanda suka dace da su tura bukatar neman aikin amma dole masu nema su kasance daga cikin masu shaidar rijistan da karanta ilimin Ingozoma, CHEW da JCHEW.
Kazalika, dole ne mai bukatar a daukeshi aikin dole ya kasance na da shaidar samun gwaji kuma a shirye yake ya yi aiki a ko’ina a sassan jihar.
Sannan, masu neman aikin su tura bukatar neman aiki tare da kwafi na dukkkanin takardun da suka dace, addireshin email, lambar waya gami da aikewa zuwa ga ofishin babban sakataren mai cikakken iko na hukumar lafiya a matakin farko ta jihar (SPHCDA) da ke lamba 3, Yaya Arabi Close, GRA Gombe, jihar Gombe.
Kana, za a bude amsar bukayar neman aikin daga ranar 13 zuwa 26 ga watan Yulin 2022.