Hafsasn hafshoshin sojin Nijeriya, Lafatanar Janar Farouk Yahaya, ya umarci dakarun sojin kasa da ke yakar ‘yan ta’adda a kasar nan, da su ci gaba da zama a cikin shirin ko-ta-kwana, musamman don a magance kalubalen rashin tsaro.
Farouk ya sanar da hakan ne a garin Maiduguri a yayin liyafar cin abincin babbar Sallah da aka shirya wa dakarun da ke yakar ‘yan ta’adda a Arewa maso gabasa.
Shugaban wanda ya bayyana hakan ta bakin shugaban sashen tsare-tsare da shirye-shirye na sojin kasa, Majo Janar Andrew Omozoje, ya bai wa dakarun tabbacin cewa, rundunar a shirye take don ta kara habaka jin dadi da walwalar dakarun da kuma ci gaba da kula da lafiyar iyalansu, musamman wadanda ke da bukatar gaggawa.