Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin hangen nesa kuma mataki mafi dacewa da cancanta.
Zulum ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labaru wadda ya sanya wa hannu kuma aka raba wa ‘yan jaridu, da yammacin ranar Lahadi a birnin Maiduguri.
- Goron Sallah: Shugaban APC Ya Yi Wa Nijeriya Addu’ar Zaman Lafiya
- Buhari Zai Inganta Harkokin Tsaro Kafin Karshen Wa’adin Mulkinsa —Malami
“Yau na yi matukar farin ciki dangane da muhimmin labarin sanarwar da ta riskeni cewa shugabana abin koyi, inda dan takarar shugaban kasarmu a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zabi Sanata Kashim Shettima matsayin mataimakinsa. Wanda ko shakka babu wannan shi ne babban burin da nake da shi na ganin Sanata Kashim Shettima ya samu wannan dama wadda ya cancanta kuma ya dace, a matsayin daya daga cikin shugabani masu kishin Nijeriya a zukatansu.”
“A wajena, kuma ina da tabbacin kaso mai yawa a cikin shugabanni da ‘yan jam’iyyar APC, sun yi na’am da wannan hangen nesa wanda Tinubu ya yi na zabo Sanata Kashim Shettima a daidai wannan lokaci na bukatar hakan.”
“Zabar Shettima al’amari ne wanda ya shafeni a kashin kaina, tare da shugabaninmu hadi da baki dayan masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar APC, wanda nake da tabbacin cewa zamu tashi tsaye haikan, mu yi aiki tukuru, babu dare ba rana wajen yakin neman zabe domin samun gagarumar nasara a zaben 2023, in Sha Allah.”
“Bugu da kari, ko shakka babu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi dacen zaben shugaba nagari, ya zabi mutumin da ya san Nijeriya ciki da bayanta tare da kalubalen da take fuskanta. Wanda a cikin kabilun da suke jihohin Nijeriya 36 hadi da Abuja, babu wanda Sanata Kashim Shettima ba zai gaza yin gamsasshen bayani a kansa ba. Saboda yadda yake da masaniya kan yanayin mu’amalarsu ta rayuwa, al’adu, addini, tsarin tattalin arziki, da tsarin siyasarsu- a dukan wadannan jihohi 36 hadi da Abuja.”
“Shettima hakikanin dan kishin kasa ne, wanda ya yi imani kan hadin kan kasa, tare da tabbatar da hakan a wurare daban-daban a rayuwarsa.”
“A hannu guda kuma, abu mafi muhimmancin dai shi ne, Tinubu ya yi zaba wa Nijeriya mataimakin shugaban kasa mai zuwa, in sha Allah, wanda kuma hakan mataki ne na hangen nesa tare da amfani da ilimi kuma a cikin cancanta, kuma hakan zai habaka ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, duniya ma sai ta shaidi hakan.”
“Ina da abubuwan fada masu yawan gaske dangane da Sanata Kashim Shettima, amma na takaice su har sai lokacin yakin neman zabe.”
“A hannu guda kuma, zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana jinjina da girmamawa ga shugaban jam’iyyar mu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa kyakkyawan shugabancin da ya gudanar a cikin wadannan shekaru tare da cikakken goyon bayan zaben Sanata Shettima ya marawa dan takarar shugaban kasa.”
“Har wala yau kuma muna yaba wa shugabanin majalisar zartaswa na kasa a jam’iyyar APC tare da mambobin kwamitin kwararru da dattawanmu na jam’iyyar hadi da ilahirin masu ruwa da tsaki a gudanar da jam’iyyar APC.”
“Muna yaba wa jajircewar baki xayan Gwamnonin APC a kararshin jagorancin babban yayana, Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu.”
“Haka zalika da dukan shugabanin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a Arewa Maso Gabas bisa cikakken goyon bayansu, shugabanin jam’iyyar APC a jihar Borno da dimbin magoya baya, muna matukar godiya.” Gwamna Zulum.