Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta ce tsohuwar ministar jin kai ta Nijeriya, Sadiya Umar Farouq ba ta ƙi amsa gayyatarsu ba, kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN a ranar Alhamis a Abuja.
- Asalin Yadda Aka Samo Sunan Hausa Bakwai Da Banza Bakwai
- Tinubu Ya Bukaci Ma’aikatu Su RIka Fitar Da Rahoton Kasafin Kudi Duk Wata
Ya ce, da gaske ne ba ta je ofishinsu ba a lokacin da suka gayyaceta, amma ta aike musu da wasiƙar cewa, ba za ta samu damar zuwa ba saboda uzurin rashin lafiya da take fama da shi.
“Da gaske ne ba ta zo ofishinmu ba amma kuma ta tura mana wasiƙa kan cewa ba ta da lafiya, sannan kuma ta tura Lauyanta da ya wakilce ta a Hukumar tamu” inji shi.
Tun da farko, Dele ya ce, Halima Shehu wacce ta yi aiki a karkashin ma’aikatar jin kai da Hajiya Sadiya Umar Farouq ta rike a mulkin gwamnatin Buhari, tuni hukumar (EFCC) ta sallame ta bayan ta gayyace ta a ranar Talata, amma da sharadin za ta rika zuwa hukumar lokaci zuwa lokaci domin ci gaba da gudanar da bincike.