A wani yunkuri na tabbatar da tsarin kasafin kudi mai inganci, Shugaba Bola Tinubu ya umarci dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su rika fitar da rahoto duk wata kan yadda suka aiwatar da kasafin kudin 2024.
Da yake jawabi a wurin rattaba hannun a fadar shugaban kasa, a Abuja, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, gwamnatinsa za ta rinka bibiyar aiwatar da kasafin kudin na Naira tiriliyan 28.7 cikin tsanaki tare da sanya ido a kai.
- Juyin Mulki: Faransa Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Na Nijar
- Zargin Sata: Jami’an ‘Yansanda A Kaduna Sun Kama Buhunan Taki Guda 600
Ya zayyana muhimman matakan da za a bi don tabbatar da bin ka’ida da inganci wajen aiwatar da kasafin kudin.
“An umarci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati su sani cewa, suna da nauyi da ya rataya a kansu na bayar da rahoton ayyukan kasafin kudi wata-wata ga ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki, wanda kuma zai tabbatar da sahihancin hakan,” in ji shugaba Tinubu.
Don kara inganta sa ido tabbatar da tabbatar da nasarar aikin, Shugaban kasar ya sanar da cewa, Ministan Kudi da na Tattalin Arziki za su rika yin bita akai-akai.
Kazalika, Shugaba Tinubu ya tabbatar da aniyarsa ta ganin nasarar tsarin ta hanyar jagorantar tarukan majalisar hadin kan tattalin arziki lokaci-lokaci.
Kasafin kudin shekarar 2024 mai taken ‘kasafin kudin sabunta fata’ ya ware kudade ga muhimman fannonin da za a fi ba da fifiko, da suka hada da tsaron cikin gida, samar da ayyukan yi, daidaita tattalin arzikin kasa, ingantaccen yanayin saka hannun jari, bunkasa jari, rage talauci, da samar da zaman lafiya.
Shugaban ya yi gargadi ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan rahoton da ake bukata daga gare su.
“Ina so tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, an gargadi dukkan hukumomi da ma’aikatunmu da cewa, idan ba za su iya aiwatatar da ayyukan gwamnati bisa inganci, sadaukarwa da amana ba, to lallai ya fi musu su tafi su bar aikinmu mu yi a madadin su.”