Kamfanin ALX Nigeria ta yaye masu kirkirar fasaha sama da 1,000 a cikin shirinta na shekarar 2023 tare da shan alwashin jan damara wajen cigaba da nemo mafita ga matsalar da Nijeriya ke fuskanta na marasa aikin yi.
Da ta ke jawabi a wajen bikin yayen wanda ya gudana a Legas, Ruby Igwe, manajan ALX a Nijeriya, ta bada tabbacin yunkurinsu na bai wa ‘yan kasuwa masu tasowa dabaru da hikimomi kan amfani da fasaha da hakan zai taimaka sosai wajen bunkasa cigaban tattalin arzikin kasar nan da kuma habakarta.
Ruby Igwe, ta kuma jinjina ma wadanda aka yayen bisa jajircewarsu wajen koyon abubuwan da ake son su koya a karkashin shirin.
- Kasafin 2024: Tinubu Ya Umarci Ma’aikatu Su Rika Ba Da Rahoton Ayyukansu Duk Wata
- Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kudiri 120 Cikin Wata Shida – Hon. Tajudeen
“ALX ta maida hankali wajen koyarwa da bada tallafin karatu. Kun kasance a nan ne saboda jajircewarku da himmarku.
“Afrika na fama da matsalar matasan da ba su yi karatu ba da marasa aikin yi. ALX Nigeria da Africa sun dukufa wajen ganin sun tallafa wa matasa miliyan uku da kwarewa a bangaren fasaha da zai yi hayar taimakonsu a ayyukansu na gaba da kasuwancinsu,” ta shaida.
Ta taya wadanda aka yayen murna da basu tabbacin samun goyon baya da tallafi a kowani lokaci, “kungiyar nan za ta cigaba da kasancewa a nan domin ku, kuma za mu tunkari matsalolin da za ku fuskanta a tare hanaki daya. Sannan, za mu kasance masu baku shawarori daga kwararrun masana da dauraku a hanyoyin da suka dace domin rayuwa ta ke inganta.”
Aledandra Edem, daya daga cikin wadanda aka yaye ta bayyana yadda ta samu horon, “wannan horon shi ne irinsa na farko da na fara na kammala ba tare da ciwon kai da shan wahala ba. A lokacin da ka shiga koyon a wasu wuraren, za ka ji koyon bai dace da kai ba. Amma a nan mutum zai gamsu har ma ya samu cikakken horon da ake son ya koya da shirin samun damar makin ayyuka.”
Wata karin wacce aka yaye, Temitope Nelson, ta ce, “baya ga kwarewar da muka samu a bangaren fasaha, gidauniyar ta kasance cibiyar koyar da yadda mutum zai samu gogewa wajen hada manhajoji. Na koyi yadda zan tafiyar da abubuwan da kaina da wasu, zan iya kasancewa mai dogaro da kaina na kuma taimaki wasu.”