A shekarar 2023 da muka yi ban-kwana da ita, kasashen Sin da Afirka sun samu moriyar juna. An samu sakamako mai kyau a hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. Baya ga kyakkyawar mu’amalar tsakaninsu, kasar Sin ta dage wajen sada zumunta da kasashen Afirka, ciki har da kasar Benin.
Sanin kowa ne cewa, dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Benin tana da zurfi sosai. Tun bayan da aka kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu a shekarar 1964, cikin shekaru kusan 60 da suka gabata, a ko da yaushe bangarorin biyu suna abokantaka tare da nuna sahihanci, wanda ya zama wani misalin hadin gwiwar kasashe masu tasowa a fannin mutuntawa gami amincewa da juna. A cikin shekarar da ta gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Benin ta kai wani sabon matsayi, wadda ta sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Benin, har da Sin da kasashen Afirka, da kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga kasar Sin da kasashen Afirka a sabon zamani.
- Safarar Yaran Bauchi A Kano: Yadda Aka Sace Diyata ‘Yar Shekara 5 Daga Aiken Ta Shago –Malam Mukhtar
- Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 4 Na Binciken Yanayi Samfurin Tianmu-1
Yayin da kasar Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje, ana samun karuwar baki musamman ma daga kasashen Afirka dake zuwa kasar Sin domin yin karatu da kuma aiki. Suna shiga cikin sassan kasar Sin tare da gane ma idanunsu yadda kasar Sin ta samu ci gaba a cikin ’yan shekarun baya. A tunaninsu, mene ne ainihin dalilin ci gaban kasar Sin? Wani dalibi mai suna Bodjrenou Mahoudjro David daga kasar Benin ya ba mu amsa.
A matsayin wani dalibin ketare dake karatu a kasar Sin, David ya dade da zama tare da yin karatu a kasar Sin, ya kuma kwashe shekaru da yawa yana neman ilimi, tun daga matakin digiri na farko har zuwa digiri na uku a kasar Sin, kamar yadda dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Benin ta ci gaba da bunkasa fiye da rabin karni. David ya karanta fannin ilimin aikin noma a jami’ar aikin noma da ilmin gandun daji ta Fujian, kuma yana fatan wata rana zai samu damar yayata ilmi da fasahohin da ya koya a kasar Sin a kasar Benin, domin bunkasa ci gaban aikin noma na kasarsu.
Har yanzu David yana tunawa da abin da ya faru yayin da ya iso kasar Sin yau shekaru 11 da suka shige. Kasar Benin dake yammacin Afirka tana da nisa sosai da kasar Sin, kuma yanayin muhalli da abinci sun sha bamban da kasar Sin. Ga David, wanda bai taba koyon Sinanci ba kafin ya zo kasar Sin, yin karatu a kasar, zabi ne mai cike da jarumta. David ya ce, wannan shawara ce da ya yanke tare da iyalansa duka. Ya ce haka, “A wata rana iyayena sun buga mini waya cewa, an zabe ni cikin wadanda za su yi karatu a kasashen ketare da kasarmu ta gudanar. Haka kuma iyayena sun gaya min cewa, dukkan iyalaina sun yanke shawara bai daya, wato idan ina so, suna son in je kasar Sin yin karatu.”
A karatun digiri na farko, David ya zabi karanta fannin aikin noma, kana a digiri na uku, ya karanta kimiyyar abinci. A cikin shekaru 11 da ya kwashe yana zama a kasar Sin, David ya je biranen kasar Sin da yawa kamar Chongqing, da Hangzhou, da Quanzhou da sauransu. Kuma ya taba gudanar da aikin sa-kai na koyar da dalibai dake wani kauye a lardin Fujian. A matsayinsa na dalibi mai koyon ilimin aikin noma daga kasar Afirka, David yana da nasa ra’ayi game da kauyukan kasar Sin, inda ya ce, “A kasarmu, akwai kauyuka masu yawa da babu wutar lantarki, amma kusan dukkan wurare a kauyukan kasar Sin suna da wutar lantarki. Kuma bisa manufar farfado da yankunan karkara, ina jin cewa, ci gaban yankunan karkara na kasar Sin ya karu sosai a yanzu.”
A jami’ar aikin noma da ilmin gandun daji ta Fujian inda David yake karatu, akwai wani shahararren manazarci mai suna Prof. Lin Zhanxi, wanda ya kirkiro fasahar noman Juncao. Duk da cewa, David ba dalibin farfesa Lin ba, amma ya sha shiga aikin tallata fasahar noman Juncao yayin da yake karatu a jami’ar, inda yake yiwa dalibai daga kasashe masu tasowa dake samun horon fasahar noman Juncao, aikin fassara ko tafinta daga Sinanci zuwa Faransanci. A cikin wadannan shekaru ke nan, David ya gane ma idonsa yadda wannan fasaha mai inganci ta karade sassan duniya. Ya ce, “Fasahar noman Juncao ta amfani kasashe masu tasowa matuka. Dalibai daga irin wadannan kasashe da suka zo kasar Sin don samun horo, sun koyi fasahohin shuka ciyayin Juncao, kuma mun ci gaba da tuntubar juna, bayan sun koma kasashensu. Sun gaya min cewa, sun shuka ciyayin Juncao a kasashensu kuma sun sami fa’idodin tattalin arziki sosai yayin amfani da fasahar nan.”
Aikin noma shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar Benin, wanda ya kai fiye da 1/3 na GDPn kasar. Daga digiri na farko zuwa na uku, David ya canza fannin karatunsa daga aikin noma zuwa kimiyyar abinci, saboda yana so ya ba da gudummawa ga ci gaban aikin noman kasarsa a nan gaba. Ya ce, “Da farko, na koyi aikin noma, abin da na yi tunani shi ne, yaya za’a yi domin kara samar da hatsi, daga bisani sai na yi tunanin yaya za a sarrafa hatsin, bayan an girbe shi. Saboda aikin noma shi ne tushen tattalin arzikin kasata, amma hanyar sarrafa hatsi a kasarmu, tana fuskantar koma baya, abun da ya sa nake so in koyi matakan noma na zamani, wato tun daga shukawa har zuwa sarrafa amfanin gona, saboda haka na canza fannin karatuna daga aikin gona zuwa kimiyyar abinci.”
A ko da yaushe gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan gudanar da hadin gwiwar aikin noma da kasar Benin. Cibiyar baje kolin fasahohin aikin noma ta Sèmè-Kpodji da kasar Sin ta samar a kasar Benin, wadda ta fara aiki a watan Satumba na shekarar 2010, na daya daga cikin ayyuka 14 na farko da aka samar a kasashen Afirka, bayan taron koli na Beijing na hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2006, kuma aikin ba da agaji na farko da kasar Sin ta aiwatar a Afirka. A watan Disambar shekarar da ta gabata, an bude bikin baje kolin koyar da amfani da injunan sarrafa auduga kashi na uku na kasar Sin da Benin a shekarar 2022, inda a ranar 9 ga watan Agustan wannan shekara, aka gudanar da bikin bude taron koyar da fasahohin noman masara a kasar Benin a shekarar 2023, a cibiyar nuna fasahohin aikin noma ta kasar Sin da Benin……David ya ce, ganin babban sakamakon da aka samu a fannin hadin gwiwar aikin noma tsakanin kasashen biyu, yana sa ran zai yada ilmi da fasahohin da ya koya a kasar Sin a Benin, domin inganta ci gaban aikin noma na kasarsa. Ya ce, “Ta fuskar fasahar aikin noma, fasahar Sin ta sha bamban da fasahar gargajiyar kasarmu, kuma dole ne mu sauya zuwa sabon salo. Alal misali, ta fuskar amfani da takin zamani, manoma da yawa ba su kware wajen amfani da shi ba, wannan ya sa yawan amfanin gonan da ake nomawa a kasarmu ya ragu sosai, kuma har yanzu ana bin hanyar gargajiya wajen shuka hatsi, don haka gabatar da fasahar kasar Sin ga kasata, wata kyakkyawar dama ce wajen samun ci gaba.”
A shekarar 2022, an taya murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomassiya tsakanin kasashen biyu. Kuma a ranar 31 ga watan Agusta zuwa ranar 3 ga watan Satumba na shekarar 2023, shugaban kasar Benin Patrice Guillaume Athanase Talon ya kawo ziyarar aiki kasar Sin bisa goron gayyatar da aka yi masa. Kafin wannan ziyara, shugaban Benin ya sha yaba hanyar ci gaba da kasar Sin ta zaba da kanta. A ranar 1 ga watan Satumbar 2023, a lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaba Talon na Benin, shugabannin biyu sun sanar da cewa, kasashensu sun kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
A matsayinsa na dalibin da ya kwashe tsawon shekaru 11 yana zaune a kasar Sin, David ya ce, yana fatan zamanintarwa irin ta kasar Sin, za ta taimaki kasashe masu tasowa da yawa don samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. Ya ce, “A ganina, zamanintarwa irin ta Sin, ba ci gaba ne a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha kawai ba, har ma tana da ma’ana ga gado gami da inganta al’adun gargajiya, wadanda suka zama muhimman bangarori a cikin zamanintarwa irin ta Sin. Ina fatan kasata da sauran kasashe masu tasowa, ba salon kasar Sin kawai za su koya ba don samun ci gaban tattalin arziki, har ma ya kamata su maida hankali wajen bunkasa da kuma gadon al’adunsu.”
Labarin David abin koyi ne na sada abokantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka. Akwai kuma matasan Afirka da dama, wadanda suka zo kasar Sin dake fatan cimma wasu burukansu, ba kawai fatan samun ilimi a kasar Sin ba, har ma suna inganta dangantakar dake tsakanin kasashensu da Sin.
Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, ita kuma Afirka nahiya ce dake mafi yawan kasashe masu tasowa, Sin da kasashen Afirka a ko da yaushe su kasance al’umma mai makoma bai daya. A cikin sabuwar shekara, Sin da kasashen Afirka na gab da shiga wani sabon zamani na gina al’umma mai makomar bai daya a tsakaninsu. (Safiyah Ma)