A tattaunawar shafin Adabi da marubuci ZAKIYYA M. DAHIR wadda aka fi sani da ZEE MD, ta bayyana wa masu karatu yadda ta sha gwagwarmayar fara rubutu da kuma irin rubutun da ta fi sha’awa wanda jigonsa yake kasancewa na tsangwamar mutum amma daga bisani kuma abin ya zama masa alheri. Akwai sauran abubuwa a cikin hirar tare da PRINCESS FATIMA ZAHRA MAZADU kamar haka:
Ko za ki fara da bayyana wa masu karatu cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki?
Da farko dai sunana Zakiyya M. Dahir wacce aka fi sani da Zee MD. An haife ni a garin kano, nayi karatuna tun daga firamare har zuwa sakandare, daga nan na juya bangaren karatun islamiyya nayi saukar alkur’ani me girma tare da sauran littattafan Addini, daga nan kuma nayi aure.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutu?
A gaskiya abin da ya ja hankalina game da rubutu shi ne; ina son in isar da sakonnin da mutane za su amfana da shi, kuma Alhamdulillah nayi nasarar yin hakan.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Alhamdulillah gwagwarmaya kam an sha ta sosai, don duk abin da za ka fara a rayuwa dole za ka fuskanci kalubale, musamman da farko tunda ba iyawa kayi ba, amman Alhamdulillah yanzu komai ya wuce.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu kina sha’awar fara rubutu, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
A gaskiya ‘Yan uwana da iyayena da kuma jigona wato mijina, sun karfafa min gwuiwa akan rubutuna ban samu matsala dasu ba, koda yaushe tsakaninmu fatan alkairi ne da kuma addu’ar samun nassara.
Ya farkon fara rubutunki ya kasance?
Farkon fara rubutu na ban sha wahala ba saboda daman ina karatun littafi, sai dai ta bangaren yadda zan saita alkalamina wajen tantance harufan rubutu da kuma saka aya da alamar tambaya nasha wuya kafin na gano.
Kamar wanne bangare ki ka fi maida hankali akai wajen yin rubutun?
Na fi maida hankali akan rubuta labarin da zai nuna an tsangwami mutum, amman a karshe da ya yi hakuri sai hakurin ya yi masa amfani har ya zamo shi ne ake son a gani.
Daga lokacin da ki ka fara kawo i-yanzu kin rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?
Daga lokacin dana fara rubutu zuwa yanzu na rubuta labarai sun kai goma, kuma ma sha Allah ba laifi sun samu karbuwa a zukatan Al’umma.
Ko za ki iya fadawa masu karatu sunayensu?
Na Rubuta littafai guda Tara ; Makircin cikin gida, ‘Yar kishiya, ‘Yar Hannu, Mawakiya, Ni Bora ce, Rayuwa Biyu, Nafi k’arfin Talaka, Atare muka taso, Bazawara ce, yanzu kuma ina rubuta ‘Zawarcin Aliya’
Cikin labarun da kika rubuta ko akwai wanda kika buga?
Har yanzu ban buga labari ba, sai dai in Allah ya nufa nan gaba ina sa ran bugawa.
Wanne ne ya zamo bakandamiyarki cikin rubutun da ki ka yi?
Duk littattafaina Ina sonsu, amman wanda ya zamo bakandamiya ta shi ne ‘Akwai Kura’.
Wanne labari ne rubutunsa ya fi baki wuya?
Littafin ‘Rayuwa Biyu’ gaskiya ya ban wuya dan sai da na ji kamar ma na hakura saboda wuya, sai kuma dai na jajirce har nayi nassarar kammalashi, shi ne a ciki littattafaina ya zo da sabon salo shiyasa na sha wuyar sa.