Bayan kai wani hari da ya yi sanadin kashe wani jigo na kungiyar Hamas a Beirut da Isra’ila ta yi, kasashen duniya na ci gaba da kiraye-kirayen a kai zuciya nesa bisa fargabar barkewar yaki a karin sassan gabas ta tsakiya.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi gargadi game da duk wani shiri na kai hari a Lebanon, a lokacin da yake Magana ta waya da Benny Gantz, mamba a majalisar ministocin yakin Isra’ila.
- Mahara Sun Halaka Wasu ‘Yan Kasuwa 8 A Katsina
- Wace Alkibla Taron Magance Shan Kwaya Na Katsina Ya Dosa?
Gwamnatin Lebanon ta zargi Isra’ila da neman kyasta wutar yaki a gabas ta tsakiya, bayan wani harin bam da ta kai Birnin Beirut da ya kashe Mataimakin Shugaban kungiyar Hamas Saleh Al’arori.
Wakiliyar BBC ta ce Firaministan Lebanon Najib Mikati, ya ce Isra’ila na so ne ta janyo Lebanon cikin yakin, wanda hakan ihu bayan hari ne, da zummar karkatar da hankalin duniya daga kan kayin da ta sha a ranar 7 ga watan Oktoba.
Saleh al-Arouri, ya rasa ransa da wasu manyan kwamandojin Hamas yayin harin na jirgi marar matuki.