Wata Gidauniyar bunkasa shugabanci da ake kira da Glovis a karkashin shirinta, ta tallafa wa zawarawa 500 da kuma dattawa 10 da kayan abinci a Jihar kaduna.
Da yake mika kayan da kudaden, Shugaban Gidauniya Mista Kayode Akinade ya ce, an raba wa wadanda suka amfana da ne don nuna jin-kai a gare su.
- Adadin Kudin Musaya Da Sin Ta Adana Ya Kai Dala Biliyan 3238 A Karshen Bara
- Babban Jami’in Diplomasiyyar Sin Ya Takaita Abubuwan Da Hadin Gwiwar Sin Da Amurka Ya Kawo
Kayode ya kara da cewa, wadanda suka amfana an zabo su ne daga jihohin Kaduna, Kwara, Oyo, Abuja, Kano, Nassarawa, Filato, Benin, Binuwe da Legas.
Ya ci gaba da cewa, kayan da aka raba masu sun hada da; buhunhunan shinkafa kudi da sauransu.
Kazalika, Kayode ya sanar da cewa, a lokacin bukukuwan kirsimeti na da na shekarar data gabata, zawarawa da 330 da aka zabo daga jihohi bakwai suka amfana da tallafin gidauniyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp