Wata mata da ba a san ko wace ce ba, ta sace wani jariri a ranar Talata a Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafia a Jihar Nasarawa.
Lamarin sanya mahaifiyar shiga cikin damuwa da bakin ciki.
- Dan Majalisa Ya Koka Kan Yawan Garkuwa Da Mutane A Kogi
- Babu Farfesan Bogi A Jami’ar Bayero Ta Kano – Shugaban Jami’a
Misis Wosilat Suleiman, mahaifiyar jaririn, ta haifi danta ne asibitin.
A cewar wata ‘yar uwar mai jegon da ke taimaka mata ta ce ta gabatar mata da wata da za ta zauna da ita kafin ta dauko wani abu ta dawo.
“Da farko na dauka matar na da majinyaci a dakin ne ban yi tunanin sata ta zo ba,” in ji Misis Suleiman.
“Matar ta bukaci yi wa jaririn wanka, daga tafiya muka neme ta muka rasa.”
Mai jegon ta roki hukumomi da su taimaka mata wajen gano yaronta da aka sace.
Hukumar kula da asibitin ta yi matukar damuwa kan faruwar lamarin, inda ta kuduri aniyar tsaurara matakan tsaro a asibitin.
Dokta Mohammed Salihu, mukaddashin shugaban masu kula da lafiyar mata a asibitin, ya tabbatar da cewa wannan shi ne karon farko da irin hakan ta faru a asibitin.
Ya bayyana cewa an haifi jaririn Misis Suleiman da misalin karfe 3 na dare kuma da farko an damka wa danginta amana kafin a tura su sashen kula da masu haihuwa.
Dakta Salihu ya tabbatar wa jama’a cewa asibitin na bai wa ‘yansanda cikakken hadin kai don ganin an damke matar.
Ya bayyana cewa an tsare ‘yar uwar mai jegon don yi mata tambayoyi, kuma wasu ma’aikatan da ke bakin aiki a lokacin da lamarin ya faru su ma suna taimakawa wajen binciken.
Bugu da kari, ya yi alkawarin yin nazari kan faifan bidiyon na’urar CCTV ta asibitin don taimakawa wajen gano mai laifin.