• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tattalin Arziki Mai Alaka Da Fasahohin Zamani Na Samun Ci Gaba A Kasashen Afirka

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Fannin tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani ya shafi zaman rayuwar dukkanmu.

Duk wani lokaci da muke biyan kudi da wayar salula, ko kuma sayen kayayyaki ta kafar yanar gizo na Internet, muna samar da gudunmowa ga ci gaban wannan fanni na tattalin arzikin.

  • Maimakon Maimaita Bukatar “Samarwa Kai Kariya” Kamata Ya Yi Amurka Ta Nazarci Ainihin Dalilin Kafa Huldar Diflomasiyya Tsakanin Ta Da Sin

Yanzu haka, wannan bangaren tattalin arziki na samun ci gaba cikin matukar sauri a kasashen Afirka. Idan mun dauki bangaren kasuwanci ta kafar shafin Internet a matsayin misali.

Sin

Mutanen da suka sayi kaya ko kuma suke yin ciniki ta kafar Internet sun kai miliyan 233 a kasashen Afirka a shekarar 2019, adadin da ake sa ran ganin karuwarsa zuwa miliyan 478, zuwa shekarar 2024.

LABARAI MASU NASABA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Wannan yanayi na samun ci gaba ya burge mutanen duniya, kana wani abun da ya fi sa ni murna, shi ne yadda fasahohi na kasar Sin ke taka muhimmiyar rawa a ciki.

A kasar Kenya, mutane sun fara yin amfani da manhajar da ake kira “Mobile Wallet” wajen biya kudi a shekarar 2007.

Wannan manhajar ta sa mutane suna iya biya da karbar kudi, ta hanyar tura sakon text, ko da kuwa wayoyin salularsu ba na zamani ba ne. Sai dai, wannan fasaha ta gamu da matsala a shekarar 2012: Yadda ake samun dimbin mutane masu yin amfani da manhajar ya sa aka kasa tafiyar da ita yadda ake bukata, inda aka fara gamuwa da matsalar karbar kudi duk ranar Juma’a.

Don daidaita wannan matsala, an gayyaci wani kamfanin kasar Sin, wanda ya taimaka wajen inganta manhajar zuwa wata da ba za a sake gamuwa da matsala yayin da ake amfani da ita ba, har ma an kara wasu hidimomi na sayen tikitin jirgin sama, da na kasa a ciki. Zuwa yanzu, manhajar “Mobile Wallet” ta samu mutane masu yin amfani da ita kimanin miliyan 30 a kasar Kenya, da sauran wasu fiye da miliyan 20 a kasashen Tanzania, da Ghana, da Masar, da dai sauransu.

Hakika muna iya ganin yadda hadin gwiwar Afirka da Sin ke tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani a kasashen Afirka, a fannoni daban daban. Misali, a fannin kasuwanci ta kafar Internet, wani dandalin kasuwanci da wani kamfanin kasar Sin ya kafa, yana taimakawa wajen samar da kayayyaki na kasashe daban daban, zuwa mutane kimanin miliyan 300 na gabashin Afirka, da samar da guraben aikin yi ga mutane fiye da dubu 10.

Kana a bangaren horaswa, kamfanonin kasar Sin sun yi hadin kai da jami’o’in kasar Afirka da Kudu, wajen kafa cibiyoyin nazarin fasahohin sadarwa na zamani.

A cewar Abdullahi Usman, darektan sashen raya kayayyakin more rayuwa na hukumar raya fasahohin sadarwa na zamani a Najeriya, yanzu a wasu birane 17 dake wasu kasashe 15 na nahiyar Afirka, akwai kamfanoni fiye da 1500 da suke kokarin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin wajen shigo da fasahohi na zamani.

Yadda wadannan kamfanonin kasashen Afirka suke kokarin hadin gwiwa da kasar Sin ba zai ba mutane mamaki ba.

Kasancewar shirin raya fasahohin zamani na cikin manyan yarjeniyoyin da kasashen Afirka suka kulla tare da kasar Sin, yasa an karfafa hadin gwiwar bangarorin 2, har zuwa shekarar 2035.

Wannan shiri ya dace da manufar kasar Sin ta “koya wa mutane fasahar kamun kifi maimakon ba su kifi kawai” a fannin hadin gwiwarta da kasashen Afirka, kana zai biya bukatar kasashen Afirka ta zamanintar da fasahohi, da raya tattalin arziki.

A yanzu mun fara ganin sakamakon shirin, kana za mu ga karin nasarorin da za a samu karkashinsa a nan gaba. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
Daga Birnin Sin

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Next Post
2023: Tinubu Ya Zaɓi Kashim Shettima A Matsayin Mataimaki

Abinda Yasa Na Zabi Musulmi Mataimakina - Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.