‘Yansanda sun tabbatar da cewa mutane shida ne suka jikkata a wata arangama tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Rundunar ‘yansandan ta ce lamarin ya faru ne a ranar 6 ga watan Janairu, 2024, lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga suka yi yunkurin tsallaka babban titin, inda jami’an tsaro suka afka musu domin tarwatsa su.
- Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Shekarar 2023
- Nijeriya Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Aikin Hajjin 2024
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya fitar, rundunar ta yi karin haske kan lamarin domin warware zare da abawa a kan wani rahoto da aka bayar na sace mutane a wannan ranar a kusa da Kateri.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Audu Ali ya bukaci ‘yan jarida da su rika tantance bayanai daga hukumomin tsaro da sauran wadanda abin ya shafa kafin su wallafa.
A ranar Talatar makon nan, daya daga cikin jaridun kasar nan ta ruwaito cewa an sace matafiya a kusa da kauyen Kateri a wani samame na tsawon mintuna 45 da ‘yan bindiga suka kai a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, a ranar Lahadi tare da sace mutum 30.
Rundunar ta jaddada bukatar ‘yan jarida su rika tantance gaskiyar bayanan da suke samu a wurin jami’an tsaro kafin su kai ga bugawa.
Rundunar ‘yansandan ta ce lamarin ya faru ne a kusa da wani wuri da ake kira da Dogon Fili, kuma a yayin musayar wuta ne mutane shida suka ji raunuka daban-daban da harsasai.
“Wadanda suka jikkata sun hada da Jibrin Tasiu, Jummai Abubakar, Zafira Abubakar, AbdulKarim Nurudeen, L/Cpl Chinedu Jerry Moneke, da Ayo James. Ba tare da bata lokaci ba an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu,” in ji ‘yansandan.
Rundunar ‘yansandan ta yi kira ga al’ummar yankin da abin ya shafa da su kai rahoton duk mutumin da ake zargin ya ji rauni sakamakon harbin bindiga ga ofishin ‘yansanda mafi kusa da su.
Rundunar ta jadadda cewa abin da ya faru na da matukar ban takaici amma ta jaddada cewa a halin yanzu an kawar da barazanar da ke hanyar, matafiya na iya ci gaba da kai-komonsu lami lafiya.
Jaridar da ta bayar da labarin dai ta ce wannan ne karon farko da ‘yan bindigar suka kawo hari a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja cikin watanni 10.