A yayin da wa’adin da aka sa wa masu asusun banki na su tabbatar da sun mallaki lambar BVN da lambar NIN na katin dan kasa ke kara karatowa, akwai yiwuwar za a garkame asusun miliyoyin al’umma a fadin tarayyar kasar nan.
Idan za a iya tunawa, a ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 2023 ne Babban Bankin Nijeriya ya bayar sanarwa wa’adi inda yake umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoiyin huldar kudi su tabbatar da duk mai hulda da su ya mallaki lambar BVN da lambar katin dan kasa na NIN kafin ranar 31 ga watan Janairu na shekarar 2024.
- Mutum Dubu 29 Sun Nemi Aikin Dan Sanda A Adamawa
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Bala Mohammed A Matsayin Gwamnan Bauchi
Sanarwar ta kuma kara da cewa, daga ranar 1 ga watan Maris duk wani mai asusun ajiyar da bai mallaki lambar BVN da NIN ba za a dora wa asusun alamar ‘Post No Debit or Credit’ ma’ana ba zai iya mu’amala da asusun ba gaba daya.
Wani bincike da wata cibiya mai zaman kanta ta yi ya nuna cewa, kashi 52 (miliyan 28) na mutanen da basu da asusun banki suna da lambar NIN yayin da kashi 5 (miliyan) na masu asusun banki basu da lambar BVN ko NIN.
Binciken ya kuma nuna cewa, ya zuwa shekarar 2021 akwai masu asusun banki miliyan 191.4 a Nijeriya a ciki kuma miliyan 133.5 ke cikakken hulda dasu.
Haka kuma an samu masu BVN Miliyan 59.96 da suke da sususun banki a daidai ranar 18 ga watan Disamba 2023.
Wata daya bayan bayar da wannan umarnin, jaridar BusinessDay ta ziyarci bankuna don ganin yadda aka yi azaman cika umarnin, “Babu wani yunkuri daga masu asusun banki da basu da lambar BVN da NIN, ina ganin kamar ba a fadakar da al’umma sosai ba a kan bukatar su yi wa kansu lambobin na BVN da NIN,” inji wani manajan banki da ya nemai mu sakaya sunansa.
Shi kuwa wani ma’aikacin ‘Sterling Bank’ ya bayyana cewa, umarnin ba zai shafi yawancin masu hulda da su ba, saboda yawacinsu na da lambobin da ake bukata.