‘Yan Nijeriya sun shiga firgici biyo bayan bankado yadda gurbatattun barasa da kayan shaye-shaye ke yaduwa a sassan kasar nan da hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi (NAFDAC) ta yi.
‘Yan Nijeriyan sun nuna damuwarsu a yayin da suke ganawa da wakilanmu inda suka nuna cewa irin wadannan gurbatattun kayayyakin za su yi illa ga sassan jikinsu ba tare da saninsu ba.
- NAFDAC Ta Haramta Shigo Da Indomie Saboda Zargin Sanya Ciwon Daji
- An Gano Dukiyar Iyalan Masarautar Saudiyya Ta Fi Ta Masu Arzikin Duniya Biyu Yawa
A kwanakin baya ne NAFDAC ta gano wasu kayayyakin da ake yadawa da suke dauke da gurbatattun abubuwa a ciki da suka kunshi har da nau’ikan barasa kala daban-daban da sauran kayayyakin jabo da basu da amincewa.
Kazalika, an kuma gano cewa akwai wasu nau’ikan kayan da wa’adin amfani da su ya wuce da in aka kuma yi amfani da su za su iya illa ga jikin dan adam da suka kunshi irin nau’ikan madara, yoghurt, da wasu nau’ikan kayan shaye-shaye da sauransu.
A bisa wannan, NAFDAC ta ce, ta rufe wasu shaguna da kamfanoni bisa samunsu da fitar da jabon kaya ga al’umma wanda hakan na barazana ga kiwon lafiyar al’umma.
A bisa wannan, ‘yan Nijeriya da dama sun nuna damuwarsu da kaduwarsu kan bazuwar kayan jabo a cikin kasuwannin kasar nan.
Wata ‘yar kasuwa a jihar Legas, Mr Agatha Onome, ta ce, ta sayi madara a kasuwa amma daga baya ta gano cewa na jabo ne, “Na duba madaran da na saya bayan na dawo gida, a nan ne na fahimci cewa wa’adin amfani da shi ya jima da wucewa.”
Wani dan Nijeriya, Muhammad Adamu ya ce, “Ai ba sabon lamari ba ne yaduwar kayan jabo da gurbattatun kayayyaki a fadin kasar nan. Wasu lokutan ‘yan kasuwa ne ke yada kayan da wa’adin amfani da su ya kara domin guje wa yin asara. A maimakon su dauki yin asarar gara su maida hankali wajen janyo asarar lafiyar jama’a.
“Babban matsalar shi ne sakacin hukumomi, akwai bukatar fito da sabbin dabarun da za su kai ga magance irin wadannan matsalolin yaduwar kayan jabo a kasar nan.”
‘Yan Nijeriyan dai sun shawarci NAFDAC da ta bullo da wasu sabbin manhajojin zamani da za su tursasa amfani da su a iOS da wayoyin Android domin bada dama cikin sauki na gano kayan jabo da sahihai domin rage wa ‘yan Nijeriya firgicin da suke yawan fuskanta.
ShwagDr na cewa, “Ina ganin bullo da manhajar zai bada damar tilasta iOS da wayoyin Android domin bai wa jama’a damar bincika da sake bincika kayan da ke dauke da lambar NAFDAC a jiki.”
Kazalika, darakta-janar na NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta ce, bazuwar kayan jabo a kasuwannin kasar nan na faruwa ne sakamakon rashin ilimi, talauci da kuma matsatsin rayuwa da jama’a ke fuskanta.
Adeyeye, ta ce, hukumar ta samar da manjaha na bincikar sahihancin kaya, ta ce, “Idan kana da wayoyin zamani, za ka iya binciko code din kaya domin gano sahihancinsa ko ingancinsa.”