A wani rahoton hadaka na hasashen harkokin kasuwanci na yankin Afirka, wanda Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Duniya (FAO), tare da shirin samar da abinci na duniya (WFP) suka wallafa a kwanan baya, an yi hasashen cewa, za a samu koma baya a bangaren noman kayan amfanin gona a Nijeriya, Nijar, Chadi da kuma Mali.
A cewar rahoton, an yi hasashen tashin farashin wadannan kayan amfanin gona a daukacin wannan nahiya, a yayin kuma da ake sa ran ci gaba da kara bukatarsu.
- Bangaren Cinikayyar Waje Na Sin Ya Samu Babban Sakamako A 2023
- Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Tantuna Don ‘Yan Gudun Hijira Da Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
Kazalika, rahoton ya danganta afkuwar hakan a kan kalubalen hada-hadar kasuwancin amfanin tare da kalubalen rashin tsaro da kuma matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a wadannan nahiyoyi.
Sakamakon wannan hasashe da rahoton ya yi na samun koma baya a kan noman wadannan kayan abinci, hakan zai shafi farashin amfanin gonar kamar Masara, Alkama, Shinkafa, Gero da sauran makamantansu har nan da sama da shekaru biyar masu zuwa.
Misali, a Nijeriya idan aka yi la’akari da irin tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin kasar yake yi, rahoton ya yi hasashen samun raguwar yin noma a fadin kasar baki-daya, wanda hakan kuma zai yi sanadiyyar tashin farashin kayan abincin ya ci gaba da yin tashin gwauron zabi.
Kazalika, rahoton ya yi hasashen cewa, za a samu matukar raguwa wajen noman Shinkafa, Masara, Dawa da kuma Gero. Bugu da kari kuma, za a samu raguwar noman amfanin gona a Nijeriya da Nijar da Chadi da kuma Mali.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa, sakamakon kalubalen rashin tsaro da rikice-rikice, musamman a yankin Liptako-Gourma da kuma gabar Kogin Chadi, akwai yiwuwar a haramta fitar da kaya wanda Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka (ECOWAS), za ta kakaba wa yankunan; wanda hakan ya jawo a watannin baya kungiyar ta kakaba wa Kasar Nijar wannan takunkumi, wanda ya yi sanadiyyar dakatar da hada-hadar zirga-zirgar gudanar da kasuwanci a tsakaninsu.