Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga hukumomin shari’a da na shigar da kararraki da na kula da tsaron al’umma, su daukaka jagorancin JKS da samar da tabbaci mai karfi ga aikin farfado da kasa.
Xi Jinping ya bayyana haka ne cikin umarnin da ya bayar game da ayyukan bangarorin shari’a da na gabatar da kararraki da na kula da tsaron al’umma, yana mai kira ga mutanen dake aiki a bangarorin, da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu bisa gaskiya da halayyar kwarai.
- Kasar Sin Na Adawa Da Tilastawa Fararen Hula A Zirin Gaza Sauya Matsuguni
- Shugaban Maldives: Maldives Ta Samu Goyo Baya Daga Kasar Sin
Wannan muhimmin umarni na zuwa ne yayin da ake gudanar da taron kwamitin kolin JKS kan ayyukan bangarorin a jiya Asabar da yau Lahadi a birnin Beijing.
Cheng Wenqing, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma sakataren hukumar kula da harkokin siyasa da shari’a ta kwamitin kolin JKS ne ya gabatar da umarnin na shugaba Xi Jinping tare da gabatar da jawabi. (Fa’iza Mustpha)