Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar wasu mutane kalilan ne suka sace dukiyar Nijeriya ta hanyar amfani da tallafin man fetur cikin shekaru 40 da suka gabata.
Sai dai Tinubu ya koka da cewa ‘yan Nijeriya na tsaka mai wuya a dalilin satar.
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Yi Tsokaci Kan Yanayin Da Ake Ciki A Shiyyoyi Daban Daban
- Ranar Tunawa Da Jarumai: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu
Da yake jawabi a wajen rantsar da gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo a karo na biyu a Owerri, shugaban ya ce ya gamsu da damuwar ‘yan kasar nan, yana mai tabbata da cewa ana ci gaba da magance kalubale da sauye-sauyen da aka kawo masu matukar muhimmanci.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali sosai kan harkar ilimi da kiwon lafiya, da sauransu.
A cewar Tinubu: “A cikin shekaru 40 da suka gabata, wasu mutane kalilan ne suka dinga kwashe dukiyarmu kuma suna kiran hakan da tallafi.
“Ina tabbatar muku da cewa za a samu ci gaba mai yawa a fannin ilimi ga yaranku; zan bayar da fifiko kan masana’antu sannan kuma kiwon lafiya zai samu karin tagomashi da kulawa. Za mu horar da karin ma’aikatan lafiya,” in ji Tinubu.