Domin tunkarar kalubalen rashin tsaro, gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana duba yiwuwar kafa asusun kula da harkokin tsaro na jihar ta hanyar hada hannu da kungiyoyin kamfanoni, ‘yan kasuwa, masana’antu, kungiyoyin kwararru da sauran su don samar da kayan aiki ga jami’an tsaro.
Gwamna Uba Sani da ya ke jawabi yayin wani taron kwamitin tsaro na jihar da sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar a Kaduna ranar Talata, Gwamna Uba Sani ya ce nan ba da jima wa ba za a kafa wasu sansanoni na jami’an tsaro (FOBs) a jihar.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 2 Na Jami’ar Al-Qalam A Katsina
- Ranar Tunawa Da Jarumai: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu
Gwamnan ya ce kafa FOB din zai taimaka sosai wajen fadada yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a yankunan da ke gaba wajen fama da matsalar tsaro.
Gwamnan ya yi jan hankali ga sojoji da ‘yansanda da su kara karfin tsaro a yankin Tudun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar, saboda barazanar da ke tasowa daga yunkurin sake gina yankin bayan wani mummunan harin bam na kuskure da sojoji suka kai yankin a kwanakin baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp