Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya ce, rashin rungumar tsarin hada layukan waya da lambar shaidar dan kasa (NIN-SIM) ya bai wa ayyukan ta’addancin kwarin guiwar ci gaba da tsula tsiya, musamman garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
Ministan wanda ke ba da amsa kam tambayar da wani ya yi a shafin Tiwuta mai suna Mentus da ya yi tambayar me ya sa aka tursasa ‘yan Nijeriya zuwa hada lambar wayarsu da lambar NIM da nufin dakile ayyukan ta’addanci amma har yanzu ayyukan ta’addancin na ci gaba da wakana.
- NIS Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Kaddamar Da “Operation Tsaron Iyaka”
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
Mai tambayar ya ce me ya sa aka sanya ‘yan Nijeriya mallakar shaidar NIN? Da ba a tilasta musu ba in an san ba zai yi tasiri ba.
Tun da farko, tsohon ministan ya wallafa cewa daya daga cikin abokansa ya tara naira miliyan hamsin a matsayin gudunmawar da aka harhada domin tara naira miliyan 100 da masu garkuwa da mutane suka bukata bayan sace ‘yan mata shida a Abuja.
Ya ce, ya yi magana da mahaifin ‘yan matan biyo bayan kashe daya daga cikinsu Najeeba wacce take gab da kammala jami’a biyo bayan gaza biyan kudin fansar da mahaifin nasu ya kasa yi na biyan miliyan 60.
Pantami wanda shi ne ya kawo tsarin hada lambar NIN-SIM ya ce, kwata-kwata ba tsarin ne ke da matsala ba, illa rashin tabbatar da amfani da tsari da hukumomi da cibiyoyi suka kasa yi shi ne babban matsalar.
Ya daura alhalin rashin amfanin tsarin ga hukumomin da aka ware domin kare rayukan al’umma, inda suka yi watsi da hakan duk kuwa da cewa suna da kayan aikin da suka dace na bibiya da bin sawun masu amfani da layukan wayoyi.
“Tsarin NIN-SIM na aiki sosai. Amma, hukumomin da abun ya shafa da ke yaki da ‘yan ta’addan an bukaci su tabbatar da amfani da tsari a duk lokacin da aka aikata wani ta’addanci. Amma rashin amfani da tsarin da aiwatar da shi shi ne babban matsalar ba wai tsarin ba.
“Idan har hukumomin da suka dace ba su yi amfani da tsarin ba wajen kare rayuka da dukiyar jama’an kowani mutum to da matsala, ni na sadaukar da rayuwana na kau da kaina daga dukkanin barazanar kasheni domin tabbatar da fito da wannan tsarin,” ya shaida.