Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da fara neman gurbin aikin soji (masu digiri ) ta Intanet na shekarar 2024.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a Intanet, ta sanar da fara neman gurbin a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu, 2024.
- Manyan Kamfanonin Nijeriya 6 Da Suka Durkushe A 2023
- Matsalolin Da Za Su Dabaibaye Harkokin Masana’antu A 2024
Neman gurbin zai kare a ranar Juma’a 23 ga watan Fabrairu, 2024.
Sanarwar ta yi kira ga wadanda suke da sha’awa kuma suka cancanta su ziyarci shafin Intanet na rundunar don neman gurbin aikin.
Sanarwar ta bayyana cewa neman gurbin aikin kyauta ne.
“Duk mai sha’awar neman gurbin aikin soja na kankanin lokaci, zai iya ziyartar shafin recruitment.army.mil.ng. Kuma neman gurbin aikin kyauta ne.”
Abubuwan da ya kamata mutum ya tanada don neman gurbin aikin:
* Mafi karancin shekaru – 20
* Mafi yawan shekaru – 40
*Tsayi – 1.65
*Matakin karatu – Digiri (2.2)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp