A karshen mako ne bayani ya fito cewa, Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA ta bayyana cewa, a halin yanzu ta yi hankoron ganin ta tattara harajin fiye da Naira Biliyan 600 don bunkasa tattalin arzikin kasar a wannan shekarar ta 2024.
A karon farko, kudaden harajin da hukumar take tattara wa ya kai matuka fiye da na wani lokaci a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2023.
- Gidauniyar Agaji Ta Qatar Za Ta Gina Gidaje 500,000 Ga Marasa Ƙarfi A Kaduna –Uba Sani
- Ana Fargabar Wasu Leburori 3 Sun Mutu Sakamakon Ƙasa Ta Rufto Musu A Nasarawa
NPA ta shirya cimma wannan lamarin ne a bisa jajircewar shugaban hukumar Alhaji Muhammadu Bello-Koko, wanda ya sha alwashin ganin hukumar ta tattara kudaden shiga fiye da abin da tattara a shekarar 2023.
An kuma fahimaci cewa, hukumar gudanmarwa NPA ta sha alwashin ganin an inganta harkokin tafiyar da hukumar musamman yadda ake dubawa tare da sallamar kayyakkin da aka shigo da su don a cimma tattara wadanna kudin da aka sa a gaba.
Wani babban jami’I a ma’aikatan Sufuri wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa manema labarai cewa, Bello Koko ya samar da sabbin tsare-tsaren tattara kudaden shiga a NPA wanda hakan ya taimaka kwarai da gaske wajen kara yawan kudaden da hukumar ke zubawa a asusun kasa a shekjarar da ta gabata.
Bayani ya nuna cewa, NPA ta samar da kudaden shiga na naira Biliyan 191.4 a zangon farko na shekarar 2023 yayin da kuma ta tattara naira biliyan 200 a zangon karshe na shekarar da ta gabata.
A bayaninsa ga manema labarai, Mohammad Bello-Koko ya ce, duk da matsalar tattalin arzki da duniya ke fuskanta yadda NPA ke tattara kudaden shiga yana kara bunkasa.