An samu matsalar daukewar wutar lantarki a wasu sassan kasar Ivory Coast, inda ake ci gaba da gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023.
Wani dan jaridan Nijeriya, Suleiman Adebayo ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
- Kambun AFCON 2023: Babu Makawa Super Eagles Ta Doke Ivory Coast – Mikel Obi
- Za A Kirkiro Manhajar Bai Wa Dalibai Bashi A Nijeriya
Ya ce, katsewar wutar lantarki ba za ta rasa nasaba da barna da fusatattun magoya bayan kasar Ivory Coast suka yi ba sakamakon rashin nasarar da suka yi a hannun Equatorial Guinea da ci 4-0.
Ya ce an shafe sama da sa’o’i biyar ana ci gaba da fuskantar katsewar wutar lantarkin, lamarin da ya shafi manyan biranen kasar Ivory Coast.