Rayuwa a wasu biranen nahiyar Afirka na iya zama babban tashin hankali, musamman ganin yadda ake fuskantar hauhawar farashin ababen rayuwa, tun daga gidajen zama da kayan abinci da suke hauhawa a kullum.
Bincike ya nuna cewa, farashin kayayyakin abinci yana karuwa a kullum, hakan kuma yana faruwa ne saboda yadda farashi yake fadi tashi a kasuwannin duniya ga kuma matsalolin da ake fuskanta a bangaren aikin moma da batun samar da makamashi, wadannan da sauran dalilai ke haiifar da hauhawar farashi a kullum. Magidanta na fuskantar manyan matsaloli wajen daukar nauyin iyalansu a kullum.
- An Maido Da Huldar Diplomasyiya Tsakanin Sin Da Nauru, CMG Ta Bude Ofishinta A Nauru
- Amurka Za Ta Tallafa Wa Yammacin Afrika Da Dala Miliyan 45 Don Yaki Da Ta’addanci
Yayin da wasu kasashen Afirka suka samu bunkasar tattalin arziki, amma rashin daidato ya kasance babbar mastalar da yaki ci yaki cinyewa. Bambancin da ke tsakanin attajirai da talakawa sai kara fadada yake yi, wanda hakan yake takura wasu bangaren na al’umma tare da toshe hanyoyin tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.
Bincike na musamman da cibiyar Numbeo ta yi, ya nuna tsadar rayuwa a wasu biranen Afirka.
Ga kuma sakamnakon binciken da ke nuna birane 10 da suka fi tsadar rayuwa a Afirka, sun kuma hada da 1. Douala, Cameroon, 2. Addis Ababa, Ethiopia, 3. Harare, Zimbabwe, sauran sun hada da 4. Johannesburg, South Africa, 5. Cape Town, South Africa, 6. Pretoria, South Africa, 7. Casablanca, Morocco, 8. Rabat, Morocco, 9. Durban, South Africa, sai kuma na 10. Marrakech, Morocco.