Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan ya cire shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Uamar Ganduje tare da yawo tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Wannan lamari ya yi tsamari ne lokacin da matasan jam’iyyar APC na Jihar Kano suka bukaci Tinubu ya tabbatar ya janyo Kwankwaso a cikin jam’iyyar APC muddin yana so ya samu gagarimin goyon bayan al’ummar Kano a zabe mai zuwa.
Matasan sun yi kira da a cire Ganduje ne daga kan mukamin shugaban jam’iyyar APC sakamakon gazawar da ya yi wajen samun nasara a zaben Gwamnan Jihar Kano.
Matasan sun yi wannan kira ne a Jihar Kano lokacin wani taron manema labarai karkashin jagorancin Ali Mai Sango, inda ya bayyana cewa dawo da Kwankwaso cikin APC zai kara wa jam’iyyar tagomashi a Jihar Kano da zai iya tabbatar da cewa an samu nasara a 2027.
A cewarsa, Kwankwaso ya san duk wata lago na siyasar Kano da ma Arewacin Nijeriya gaba daya wanda zai iya tabbatar da cewa Tinubu ya samu nasarar sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu.
Ya yi ikirarin cewa Ganduje ya rasa alkiblar siyasarsa a Jihar Kano, amma idan har Kwankwaso ya dawo APC, zai daga kimar jam’iyyar zuwa wani mataki na gaba a zabe mai zuwa.
Kar Ka Dauki Wannan Shawara – Dattawan APC Na Kano
Sai dai kuma dattawan jam’iyyar APC a Jihar Kano sun siffanta kungiyar da ke kiraye-kirayen cire shugaban na jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin haramtaccen kungiya da ‘yan adawa suka kafa a jihar.
Dattawan sun bayyana cewa wannan haramtacciyar kungiya ce wanda aka kafa ta domin farfagandar siyasa mai makon mayar da hankali kan abun da ya dace, amma sun fake da kiraye-kiraye sai an cire shugaban jam’iyyar APC wanda ya shafe shekara 5 yana gwagwarmaya kan samuwar wannan gwamnati.
A cikin sanarwar da kungiyar dattawan APC na Kano suka fitar da ke dauke da sa hannun Abubakar Indabawa da Musaddik Wada Waziri bayan ganawa ta musamman, ta bukaci Shugaba Tinubu da daukacin ‘yan Nijeriya da su yi watsi da kiraye-kiraye duk wasu matasa da suke kiran a sauke Ganduje.
A cewar dattawan, a bayyana yake cewa ‘yan adawa ne suka dauki nauyin wadannan matasa domin raba kawunan mambobin jam’iyyar APC ta hanyar yin kira da a cire shugaban jam’iyyar na kasa.
Sun kara da cewa suna kiran kansu matasan APC amma ba a san su ba a jam’iyyar, kawai an dauki nauyinsu ne domin kawo radani a APC, sai dai kuma ba za su yi nasara ba.
Sun ce, “An dai dauki nauyin wadannan matasa ne domin kawo rudani a APC na yin kiraye-kiraye na sai an cire shugaban jam’iyyar wanda ya samu nasarar sasanta fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar a wasu jihohi kamar irinsu Ondo da Ribas tun lokacin da ya amshi jagoranci na tsawon wata 7.”
Dattawan sun ce wadannan matasa suna makiyan Ganduje ne saboda sun ga cewa shi kadai ne daga tsofaffin gwamnonin Arewa da ya bai wa Shugaba Tinubu kuri’u mafi rinjaye a zaben shugaban kasa a 2023.
Idan za a iya tunawa dai an fitar da wani rahoto mai cewa Shugaban kasa Tinubu ya bukaci Ganduje ya shirya da Kwankwaso da dukkan mutanen da suke shirin shiga APC.
An dai ta yada wannan rahoton ne bayan da shugaban kasa ya kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Jihar Kano bayan da kotun koli ta zartar da hukuncin tabbatar da zaben Abba Kabir Yusuf a matsayin halartaccen gwamnan Jihar Kano.
Shugaban kasan ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na Jihar Kano su kai zuciya nesa tare da tattaunawa da mutanen da suke shirin shiga jam’iyyar APC, domin samun hadin kai da kuma ci gaba jihar.
A yayin da wasu suke ganin cewa rahoton kiran da shugaban kasa ya yi wa Ganduje na sasantawa da Kwankwaso ba shi da tushe ballantana makama.
Yanzu haka dai mutane da dama sun zura na mujiya su ga ko dai Kwankwaso zai dawo APC ko kuma zai ci gaba da zama dan jam’iyyar adawa, lokaci ne kadai zai tabbatar da hakan.