Gwamnatin tarayya ta bukaci kamfanoni masu zaman kansu da su zuba jari a bangaren fasahar na’urar daukar hoto ta (Scanning) a tashoshin jiragen ruwan Nijeriya domin dorewar amfani da ita da kuma bunkasa amfani da zamani a harkokin safarar jiragen ruwa a kasar nan.
Wannan bukatar ta fito ne a wajen ganawar bullo da dabarun hanyoyin da za a inganta jiragen ruwa da samar da tsarin kara samar da kudaden shiga da aka yi a gudana a Abuja, wanda ya samu halartar ministan kula da teku da albarkatun cikin teko Gboyega Oyetola; ministan sufuri, Said Ahmed Alkali; kwanturola-janar na hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi da kuma darakta janar na hukumar kula da layukan dogo na Nijeriya (NRC), Fidet Okhiria.
- Kasashen Afirka 10 Da Za Su Samu Bunkasar Tattalin Arziki A 2024
- Bukatar Samar Da Tsaftatacciyar Adawa A Nijeriya
A wani mataki na inganta ayyukan jiragen ruwa a tashoshin jiragen ruwa da kuma ganin sun yi gogayya da takwarorinsu, ministoci da shugaban kwastam din sun amince kan cewar dole ne a samar da matakin duba jiragen ruwa na zahiri a filayen jiragen ruwa da samar da hadin guiwa da saukaka aiki domin kyautata kasuwanci.
Kudurin na kunshe ta cikin sanar hadin guiwa da kakakin ministan da kula da albarkatun tekuna, Ismail Omipidan da na kwastam spokesman, Abdullahi Maiwada.
Ministocin sun bayyana muhimmancin amfanin na’urar kimiyya ta dubawa da tantancewa wato (NIIT) wajen rage cinkoso a filayen jirage, kuma bai wa shugaban kwastam ikon tantancewa kayan da jirgin ruwa ya dauko cikin sauki da hanzari ta hanyar daukan hoton scanning cikin ‘yan mintuna sabanin hanyar da ake amfani da shi na dube-duben zahiri wanda hakan ne dauka tsowon lokaci kuma wasu lokutan ba a samun biyan bukata yadda ake so.
Don haka ne suka ce, amfani da fasahar daukan hoton zai kawo sauki sosai kuma zai taimaka wajen kyautata tsaro da rage matsatsin aiki hadi da taimaka wa kasar na sosai.
Don haka ne suka nemi masu hannu da shuni da su zuba hannun jarinsu wajen kawo na’urar daukan hotuna a filayen jiragen ruwa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sun kuma cimma matsayar cewa za a sake gina sabuwar layin dogo a gefen na’urar daukan hoto da ke filin jirgin ruwan Apapa domin tabbatar da rage cinkso da bada damar saukaka aikin daukan hoton cikin sauki da hanzari.
 Sun kuma cimma matsayar sake kwaskwarima da tabbatar da ana amfani da naurorin daukan hotuna da ake da su a halin yanzu a wasu jiragen jiragen ruwa kamar su na Apapa, Tincan Island, Onne, da PTML domin tabbatar da amfaninsu da cin gajiyarsu, kuma na’urar salula na daukan hotona su ma za a tabbatar da zuba su a muhumman filayen jiragen ruwa domin saukaka aikin duba jiragen ruwa da kayan da suka kwaso.