Shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 Dennis Francis ya godewa Sin game da dagewarta wajen goyon bayan tsarin huldar kasa da kasa karkashin jagorancin MDD. Ya kuma yabi babbar gudummawa da jagorancin da Sin take bayarwa cikin harkokin kasa da kasa.
Dennis Francis ya bayyana haka ne yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a hedkwatar MDD dake New York na Amurka a kwanan baya.
- Sin Ta Yi Nasarar Kirkirar Kwayar Halittar Nau’ikan Shanun Xizang Dake Bakin Karewa
- Sharhi: Shin Isra’Ila Za Ta Yi Biyayya Ga Hukuncin Kotun Duniya Game Da Yakin Gaza?
Ya kuma jadadda cewa, ya kamata a kiyaye kudurin babban taron MDD mai lamba 2758, da bin manufar kasar Sin daya tak. Yana mai cewa ana sa ran Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannonin inganta hadin gwiwar kasa da kasa da tinkarar kalubalolin duniya da sauransu a nan gaba.
Bisa gayyatar da ministan wajen Sin Wang Yi ya yi masa, shugaban na babban taron MDD na 78 Dennis Francis ya fara ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 27 zuwa 31 ga watan Janairu. (Safiyah Ma)