Lamarin tsaro a ‘yan kwanakin nan sun kara rincabewa, wanda hakan ya sa shugabannin rundunonin tsaro shiga tsaka mai wuya, inda al’umma ke neman karin bayani wasu kuma suna ganin jami’an tsaron basu tabuka komai ba ganin irin dinbin kudaden da ake zubawa a bangaren tsaro a kasar nan.
A kan haka ne majalisar dattawa ta gayyaci shugabanin rundunonin tsaron zuwa zauren majalisar don tattaunawa tare da nemo bakin zare.
- Zaben Cike Gurbin Makera: ‘Yan Takara Sun Yi Wa Liman Mubaya’a
- Matsalar Tsaron Nijeriya: Ku Faɗi Alkairi Ko Ku Yi Shiru!
Haka kuma majalisar wakilai ta yanke shawarar ganawa da Shugaban Kasa Bola Tinubu ganin yadda ake samun karuwar hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane a sassan kasar nan a cikin makon jiya, musamman ma hare-haren da aka kai yankin karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato inda mutum fiye da 50 suka mutu yayin da aka tabbatar da mutum 100 sun ji munanan raunuka, an kuma kona gidaje masu yawan gaske, an kuma tabbatar da rikicin ya tarwatsa mutane fiye da 20, 000 daga gidajensu, a halin yanzu suna sansanonin gudun hijira a sassan jihar.
Ana sa ran babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa; Shugaban rundunar sojin Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Shugaban Sojojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Shugaban Sojojin Ruwan Nijeriya, Cif of Nabal Staff (CNS), da kuma shugaban rundunar sojojin sama, Bice Admiral Emmanuel Ogalla sai kuma Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya Kayode Adeolu Egbetokun su bayyana a gaban majalisar inda za su bayyana wa ‘yan majalisar irin kokarinj da suke yi na magance matsalar tsaron da kuma dalilan da ya sa har yanzu abin ya-ki ci ya-ki cinyewa.
A mako mai zuwa ne za su gurfana a gaban majalisar bayan ‘yan majalisar sun dawo daga hutun mako daya da suka tafi don shiga harkokin zaben cike gurbi da za a yi a fadin kasar nan a ranar Asabar.
A kudurin da aka gabatar don gayyatar shugabanin rundunomin tsaron wanda ‘yan majalisar dattawa 109 suka sanya wa hannu sun bayyana damuwar su a kan yadda ayyukan ‘yan bindiga da kashe-kashe, da garkwua da mutane da sauran ayyukan ta’addanci suka mamaye sassan kasar nan.
Majalisa ta kuma lura da yadda ayyukan ‘yan ta’adda suka kara ta’azzara a yankin babban birnin tarayya Abuja, musamman garkuwa da mutaned da neman kudin fansa, inda sakamakon haka aka kashe mutane da dama haka kuma sun lura da yadda aka kashe wasu sarakuna gargajiya biyu a Jihar Ekiti da kuma yadda aka sace malamai da ‘yan makaranta a garin Ekiti, da kuma sauran ayyukan ‘yan ta’adda a sassan Nijeriya.
– Ana Samun Nasara A Kan Miyagun -Gwamnati
Yayin da ka yi garkuwa da wasu malaman makaranta da dalibansu a jihar Ekiti, al’umma sun harzuka inda suke nemi gwamnati ta dauki matakin gaggwa don kawo karshen lamarin. A kan haka ne shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci a gagguta ceto malaman da daliba ba tare da bata lokaci ba.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasan, Ajuri Ngelale, inda ya kara da cewa, Tinubu ya tabbatar wa da al’umma cewa, a halin yanzu ana yi wa tsarin rundunonin tsaron kassar nan garambawul ta yadda za su yi aiki yadda ya kamata.
Haka kuma shugaban kasa Tinubu ya tir da yadda aka kashe sarakuna gargajiya biyu a Jihar Ekiti, sarakuna syun hada da Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olusola, da kuma Elesun na Esun-Ekiti, Oba Dabid Babatunde Ogunsola.
Tinubu ya yi tir da kashe kashen da ake tafkawa ya kuma yi alkawarin tabbatar da hukunta wadanda suke aikata wadannan ta’asar. Ya ce, duk da mastalolin da ake fuskanta ana samun nasara a kan ‘yan ta’adda, kuma da sannu za a yi galaba a kan su.
– Masu Garkuwa Na Neman Fansar Naira Miliyan 100
A halin yanzu masu garkuwa da malamai da daliban da aka sace a Jihar Edkiti sun nemi a biya su diyyar naira miliyan 100 kafin su saki yaran da suka sacen.
Majiya na kusa da iyalan daliban suka bayyana wa ‘yan jarida a tattaunawarsu da manema labarai, sun ce masu garkwua na neman naira miliyan 10 a kan kowanne dalibi.
– Atiku Ya Sake Caccakar Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan gazawa wajen magance matsalar tsaro. Ya bukaci ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda.
Atiku ya kasance dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya dai bayyana takaicinsa ta yadda ake samun karuwar garkuwa da mutane da kuma kasha-kashe a ko’ina a fadin kasar nan.
Ya dai yi takaicin yadda aka kashe wata matashiya tare da mahaifiyarta a Abuja da kuma kisan sarakuna biyu a Jihar Ekiti a ranar Litinin.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya yi mamakin yadda shugaban kasa ya jilla zuwa kasar Faransa ba tare da daukar mataki kan ‘yan bindiga da kuma sauran ayyukan ta’addanci da ke faruwa a kasar nan.
A dai ranar Laraba da ta gabata ce, Shugaban kasa Tinubu ya zai ziyara ta musamman a kasar Faransa.
A shafinsa na sada zumunta, Atiku ya rubuta cewa, “Tinubu bai damu da halin da Nijeriya ke ciki ba na rashin tsaro. Abun mamaki fa shi ne babban kwamandar askarawan kasar nan, amma har zai iya yin wata ziyara ta musaman a wannan yanayi da ake fama da rashin tsaro a Nijeriya.
“A daidai wannan lokaci, masu garkuwa da mutane sun kashe wata matashiyar likita tare da kakarta a Abuja sakamakon gaza biyan kudin fansa na naira miliyan 90. Sannan sun kashe sarakuna guda biyu a Jihar Ekiti, dadai sauran ‘yan Nijeriyan da aka kashe da bazan iya lissafawa ba.
“Idan har matsalar ta gagare ka ne, to ka kama gife akwai masu iyawa. A halin yanzu ‘yan Nijeriya ba sa bukatar shugaba mai son shakatawa.
“Kasar nan na bukatar shugaban da zai iya aiki na tsawon awanni 24 na kowacce rana, domin magance rashin tsaro da kuma durkushewar tattalin arziki.”
– Yadda Lamarin Yake A Arewa
Masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da dan matan biyu masu shekara 16 da 14 a Kubwa da ke karamar Hukumar Bwari, birnin tarayya Abuja.
Sun nemi mahaifin yaran da ya ba su Naira miliyan 30 idan har yana son yaransa su shaki iskar ‘yanci.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 11:25 na dare.