Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da kwamitin mutum 37 a karkashin jagorancin Bukar Goni Aji da zai kasance mai shiga tsakani kan aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashi da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shettima wanda ya jagoranci kaddamar da kwamitin da ya kunshi wakilan gwamnatocin jihohi da na tarayya, bangarori masu zaman kansu da kuma kungiyoyin ‘yan kwadago.
- Tinubu Zai Kaddamar Da Kwamitin Gyaran Mafi Karancin Albashi Ranar Talata
- Sau Daya Tak Gwamnati Ta Biya Karin Albashi Na N35, 000 – TUC
Da yake magana a wajen kaddamarwar, Shettima, ya yi bukatar a yi aikin hadin guiwa da zuciya daya. Ya kuma shaida cewar akwai bukatar kwamitin ya shiga ya fita ya tuntubi kowani bangare domin samun damar tattaro muhimman abubuwan da suka kamata.
Ya kuma kara da bukatar kwamitin da su gaggauta gudanar da ayyukansu da kuma mika rahotonsu kan lokaci domin daukan matakan da suka dace.
Kwamitin shiga tsakanin an daura masa alhakin tsarawa da fito da sabon tsarin biyan mafi karancin albashi ga ma’aikata a fadin kasar nan ta Nijeriya.