Shugaban rundunar sojin saman Nijeriya, Air Marshal Hassan Bala Abubakar ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta biya su basukan da suke bi na wasu ayyuka da suka yi wa hukumar.
Abubakar ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin da tawagar INEC karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu suka ziyarci shalkwatan rundunar sojin Nijeriya da ke Abuja domin gudanar da ziyarar aiki.
- AFCON 2023: Saura Wasanni Biyu Nijeriya Ta Lashe Kofin Nahiyar Afirka
- Sojoji A Jihar Katsina Sun Fatattaki ‘Yan Bindiga Tare Da Kubutar Da Mutane
“Ina amfani da wannan dama wajen tunatar da shugaban hukumar INEC kan bashin da muke bin su wanda har yanzu ba a biya ba. Biyan bashin zai ba mu kwarin gwiwar yin aiki tukuru,” in ji shugaban sojin saman Nijeriya.
Haka kuma shugaban rundunar sojin saman Nijeriya ya ce zaben da aka kammala ya samu cikakken tsaro daga rundunar lokacin da ta yi hadin gwiwa da INEC domin samar da cikakken tsaro na rarraba kayayyakin zabe a jiragen sama a ko’ina a fadin kasar nan.
Ya ce, “Ina mai tabbatar muku cewa a shirye muke mu ci gaba da goyon bayan INEC kamar yadda muka saba yi a baya.
“Muna da issun jiragen da za su taimaka muku wajen kai kayayyakin zabe a kowani yankin kasar nan. Muna bukatar INEC ta yi gaggawar kai wadannan kayayyakin zabe domin kar a samu wasu matsaloli.”