A kwanan baya ne ministan tattalin arziki da aikin nazari kan ba da ilimi na kasar Switzerland Guy Parmelin ya zanta da wakiliyar CMG, inda ya bayyana cewa, kawo yanzu yarjejeniyoyin da kasashen Sin da Switzerland suka daddale suna amfanawa sassan biyu. Alal misali, kasashen biyu suna zubawa juna jari a bangarorin tattalin arziki da kimiyya da fasaha da sauransu, har ma suna zubawa juna jari kan aikin horaswar sana’o’i.
A halin da ake ciki yanzu, kasashen biyu wato Sin da Switzerland suna gudanar da tsarin tattaunawa a fannoni sama da 30. Ministan ya yi imanin cewa, makomar hadin gwiwar sassan biyu tana da haske, nan gaba zai dace sassan biyu su kara kyautata hadin gwiwa a fuskokin cinikayya maras shinge, da cudanya a bangarori daban daban. (Mai fassara: Jamila)