Hajiya Zainab Yakubu Muhammad gogaggiyar Ma’aikaciya, ‘Yar Siyasa, haifaffiyar Jihar Kano, Mamallakiyar Gidauniyar tallafa wa mata, musamman marayu da masu Karamin Karfi, A Tatattaunawarta Wakilinmu A Kano Abdullahi Muhammad Sheka wanda Ya samu tattaunawa da ita kan wasu daga cikin abubuwan ta na rayuwa da kuma yadda tarbiyya ta ke ada da kuma yanzu, daganan ta tabo harkokin siyasa da zamantakewar aure da kuma yadda ta hada auren da aiki.
Za mu so ki gabatar wa da mai karatu kanki?
Alhamdulillahi ni dai sunana Hajiya Zainab Yakubu Muhammad, haifaffiyar garin Kano, sai da kuma sakamakon mahaifina ma’aikaci ne kuma injiniya ne wanda ke aiki da wasu turawa masu aikin hakar ma’adanai (KUZA), wannan ta sa aiki ya kai mu Garin Jos, domin duk jejin da za su shiga shike yi masu gada, don haka na yi karatun sakandire da Jami’a duk a wajen Kano, daga baya na dawo Kano na yi digiri na na biyu a Jami’ar Bayero da ke Kano, daga nan kuma na fara aiki ina da aure kuma ina da yara, wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata.
Ya zaki kwatanta rayuwar yara ada da kuma yanzu?
Lallai wannan lamarin ba abinda za muce sai godiya, batun rayuwar yara dama sauran tsarin tarbiyya abubuwa sun matukar sauyawa kwarai da gaske, lokacin muna yara kananan duk da kasancewar iyayenmu suna da rufin asiri, amma da safe kafin mu tafi makaranta bayan mun tashi mun yi sallah mun gaida iyaye, sai a bamu sharar gida, mu goge tsakar gida lokacin ana yin wani tayil mai kala kala, sai mu sa tsumma lokacin ba a san wata Moffer ta zamani ba, haka zamu durkusa sai mun goge gida tas. Daga nan zamu shirya a kaimu makaranta, haka da yamma idan mun dawo, wadada suka dan da ta bayan dawowa daga Islamiyya za a bamu ayyuka musamman aikin abinci kasancewar mu ‘ya’ya mata gidan aure za mu tafi, ana koyawa mana girki, domin a wannan lokaci da yawa ana yi wa yara aure ka tarar ko abinci basu iya ba, amma na yanzu dadi ya yi masu yawa.
Kasancewar an samu irin waccan tarbiyyar irinta da, yanzu kuma gashi an tsinci kai a harkar aiki, ya ake hada aikin da kuma kula da harkokin gida?
Haka ake tafiyar da abubuwan gwargwadon iko saboda iyayenmu sunyi kokarin dora mu akan kyakkyawar tarbiya, mun san yadda zamu kula da aikinmu a lokacin guda muna gudanar da harkokin gida kamar yadda ya kamata, daman batun aiki wani abu ne da maigidanka yake da iko akansa, idan aka samu kyakkyawar fahimta tsakanin ki da mijainki, ba wata matsala, illa kiyi kokarin yin abubuwan da suka da dace domin tsare kimar ki amatsayinki na mace kuma matar aure sannan kuma ga irin ka’idojin da musulunci ya gidanya, har kuma yanzu gashi yara ma sun taso mun dora su akan irin wannan tarbiyyar.
Shin ko mene ya baki sha’awar tsunduma cikin harkokin siyasa?
Gaskiya akwai abubuwa masu yawa da suka sa na kalli wannan harka ta siyasa kuma nake da yakinin ganin na bayar da gudunmawar da zan iya bayarwa gwargwadon iko, akwai abubuwa guda biyu duk da na taso na tarar a gidanmu ana siyasa dukan kakannina ‘yan siyasa ne, wannan yasa na tashi da kishin siyasa sai dai siyasa bata rinjayi aiki na ba, wannan kuma yasa gashi yanzu nayi zurfi a aiki na kai wani matsayi da nake fatan samu na gama aiki na lafiya, daganan kuma idan za’a tsunduma cikin siyasar sai aduba yiwuwar hakan da yardar Allah. Abu na biyu kuma duba da yadda aka bar mata abaya a harkokin siyasa, ‘yan uwanmu na kudancin kasar nan sun yi mana nisa kwarai da gaske ta fuskar siyasa, mu yanzu musamman a arewacin kasarnan ko kansila ba’a iya amincewa mace ta tsaya takara, duk da yanzu naji ance a wata jihar an samu mace da lashe wata kujera. Amma a jihar Kano mu har yanzu bamu samun irin wannan damar ba.
Shin ko me Hajiya ke ganin ya taimaka wajen rashin samun irin wannan dama ga mata a yankin arewacin kasar nan?
Abubuwa ne da yawa, na farko mu mata muke yin zabe amma ba mu da hadin kai ko kadan, idan da zamu hada kanmu ba kujerar da ba zamu lashe ba, don haka idan da zamu hada kai har matsayin Gwamna mata na iya tsayawa duk da bana jin za a bar mana, domin anga irin wanna misali a jihar Adamawa duk da yankin Arewa ta tsakiya ne, suma sun dara mu hadin kai da wayewa ta wannan fuska, amma dai duk haka itama din wadda ta tsaya takarar Gwamna ba’a bari ta kai gaci ba.
Mene ne ya baki sha’awar shiga tsarin tafiyar Kwankwasiyya A siyasance?
Gaskiya alaka ta da tafiyar Kwankwasiyya ba yau aka fara ba, na kasance ina tare da Madugu (Kwankwaso) tun zangon mulkinsa na farko da ya zama Gwamna Jihar Kano a shekara 1999, tun lokacin ma ni bai sanni ba, kawai dai ina da ra’ayinsa domin shi ne kadai cikin ‘yan siyasar da na hakkake yana kaunara ci gaban talaka, wannan kuma bana nadamar fadin haka, domin anga yadda yake tura ‘yan’yan talkawa karatu kasashen waje, koyawa matasa sana’un dogaro, dakai, rabawa mata jari, aurar da zawarawa, kafa makarantun koyon sana’o’I iri daban da sauransu. Wannan tasa na yanke shawarar kafa kungiyar Kwankwasiyya Pillars Of Nation, wadda ta karade jihohin Kasarnna 36 harda Abuja, ba inda ba muda shugabanci, musamman mun bayar da gagarumar gudunamawa alokacin da Kwankwaso ke takarar kujerar shugaban kasar Nijeriya, kuma mu Kwankwasiyya Pillars bamu fara don mu daina ba, kasanewa tana kunshe da kyawawan manufofin da zasu taimakawa cigaban al’umma.
Mene abinda kika fi sha’awa a harkokin rayuwarki?
Gaskiya ina son naga na taimaka wa jama’a musamman mata, wannan tasa na kafa gidauniyar tallafa wa mata musamman masu karamin karfi wadda nake rokon Allah ya sawa wannan gudauniya albarka takai inda nake tsammani
Wacce Sutura Hajiya tafi sha’awar amfani da ita?
Ni bani da wata kalar sutura da nafi so, amma dai ina sha’awar tufafin irin wadanda addinin musulunci da al’adunmu na hausawa ke alfahari dasu.
A karshe wane sako kike dashi?
Alhamdulillahi babban kirana shi ne jama’a su yi kokarin kamanta gaskiya a cikin al’amuransu, sannan a yi kokarin dogaro da kai domin rashin sana’a na jefa matasa cikin mummunan yanayi, musamman babban abinda ke cimin tuwo a kwarya shi ne naga mata suna bara, wadda kuma jama’armu ta hausawa, musamman ‘yan arewa sune acikin wannan mummunar dabi’a, wanda cikin musulunci ba inda aka halasta barace barace, ina kara jinjinawa Kokarin tsarin Gwmanatin Abba Kabir Yusuf na kokarin bujiro da kyawawan tsare tsare da za su kyautata tsarin makarantun mu na tsangayu da islamiyyu wadda ake fatan suma su zama kamar yadda na zamani suke wajen takaita barace barace.
Mun gode
Nima na gode kwarai da gaske