An yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen matsalar wutar lantarki da aka sace wayoyin layukan da suka taso daga Abuja zuwa garin Jere da sauran garuruwan da ke karamar hukumar Kagarko da aka lalata su a shekarar da ta gabata.
Sarkin Shanun Jere, Alhaji Ishaq Usman Jere ne ya yi wannan kiran a hirarsa da manema labarai a Kaduna.
- Zaɓen Cike-gurbi: PDP Ta Yi Nasarar Lashe Zaɓen Kujerar Majalisar Tarayya A Jihar Jigawa
- Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Ta 2024: Maraba Da Shekarar Kwazo, Kuzari Da Nasara
Jere wanda kuma shine tsohon Manajin Darakta na kamfanin rabar da wutar lantarki, ya koka akan yadda aka bar yankin a cikin duhu biyo bayan lalata manyan wayoyin samar da wutar da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Jere.
Ya ce, lalata manyan wayoyin samar da wutar ya janyo tsaiko wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci a yankin.
Kazalika, Jere ya yi kira da a lalubo da mafita akan kalubalen rashin tsaro da Nijeriya ke ci gaba da fuskanta, inda yayi nuni da cewa, ya wajaba a kara jajircewa wajen daukar matakan kawo karshen kalubalen.
Sai dai ya sanar da cewa, gwamnatin kadai baza ta iya kawo karshen matsalar ba, sai alummar gari suma sun bayar da tasu gudunmawar.
Jere ya kuma roki alumma da su tabbatar da suna fallasa dukkan wadanda ke yiwa harkar tsaron kasar nan zagon kasa.