Kungiyar Matasan Arewa maso yamma ta nuna rashin dacewar kalaman kungiyar dattawan Katsina da suka bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya canza matakan da Gwamnatinsa ta dauka ko kuma ya rasa goyon bayan yankin a zaben 2027.
Ko’odinetan kungiyar, Alhaji Murtala Aliyu Ka’oje ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar a Sakkwato a ranar Litinin inda ya ce, ko kadan dattawan Katsina ba su da kowace irin damar kalubalantar ko wane irin matakin da gwamnatin da ke kan mulki ta dauka saboda a baya sun kasa kalubalantar matakan da ba daidai ba a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
- Cire Tallafin Fetur: Ma’aikatan Jihar Jigawa Sun Ki Amincewa Da Karin Albashin Naira 10,000
- DA ƊUMI-ƊUMI: Mata Na Gudanar Da Zanga-zanga Kan Tsananin Yunwa Da Tsadar Rayuwa A Neja
Ka’oje ya bayyana cewar duk da yawaitar asarar rayuka da dukiyoyi da tabarbarewar tattalin arzikin Arewa, babu wani dattijon Arewa daga Katsina da ya fito ya yi magana kan gurbatattun manufofin da tsohuwar gwamnati ta dauka wadanda suka illata Arewa da ‘yan Arewa.
Kungiyar datawan Katsina dai ta fito fili ta nuna rashin dacewar daukar wasu matakan gwamnati musamman dauke wasu muhimman sassan Babban Bankin Kasa da hukumar kula da filayen jiragen sama daga Abuja zuwa Lagas da kuma aikin fadada filin jirgin sama na Umaru Musa ‘Yar’Adua da ke Katsina.
“Duk da tsananin talauci, matsalolin tsaro da gallazawar siyasa da aka fuskanta a zamanin mulkin Buhari, dattawan Katsina ba su kalubalanci tsohuwar gwamnatin ba?
“Wata tambayar ita ce, yaushe ne dattawan Katsina suka zama masu sukar manufofin gwamnatin Tarayya? Mutane da dama sun rasa rayuka da dukiyoyi, sha’anin noma ya tsaya cik kamar yadda dukkanin al’amurran rayuwar al’umma suka tabarbare saboda rashin tsaro da rashin iya jagorancin Buhari amma dattawan Katsina ba su taba nuna damuwar gyara lamurran ba?”
Kungiyar ta ce ta na goyon bayan kalaman Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da ya ce wa dattawan Katsina da sauran kungiyoyi irin nasu da su ba da himma ga hadin kan kasa, su dakatar da kokarin zazafa siyasa ta hanyar kalaman da ba su dace kan Shugaba Tinubu ba.