A duk Unguwa, Gari, ko wani babban Birni da akwai wadansu mutane da turanci ana kiransu school board management committee ba karamar gudunmawa suke badawa ba wajen tabbatar da cewa makarantu suna tafiyar da harkokinsu na ayyukansu kamar yadda ya dace. Suna taimakawa ne wajen ganin makarantu suna tafiyar da ayyukansu ba tare da shiga wata matsala ba.Bugu da kari kuma su kungiya ce mai zaman kanta wadda take wakiltar al’umman makaranta da suka hada da, ‘yan makaranta, Malamai, Iyaye,Kungiyar Iyaye da Malamai, Shugabannin al’umma, har ma da sauran wadanda suke da sha’wa a kan al’amarin daya shafi ilimi.
‘Yan makaranta su gudunmawar da za su bada a nasu matsayin na dalibai shi ne su kasance masu bin dokokin da makaranta ta shimfida,ta yin amfani da su saboda yin hakan ne zai kasance sun tashi cikin da’a da maida hankali ga abubuwan da ake koya masu ta darussa cikin aji tare da wasu dabi’u wadanda za su zamar masu tamkar abokansu.Domin suma suna son watarana ace sun zama mutanen kwarai.
- Bikin Bazara Da Ke Fadada A Duniya Alama Ce Ta Mu’amala Da Fahimtar Juna Tsakanin Wayewar Kan Kasar Sin Da Wayewar Kai Daban-Daban
- Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta
Malamai su a kowane lokaci ana son su kasance baya ga ilimin da suke da shi wanada za su koyawa dalibai ta hanyar darussa abin da ya kasance kowa daga cikinsu yana da darasin da yake koyawa, dabi’unsu su zama lalle abin koyi ne wadanda daliban nasu su rika koyi da su ta hanyar aikatawa.Malamai sun kwana da sanin duk wadansu abubuwan da za su rika yi a gaban dalibansu da suka zama akasin dabiu’u nagari ba za su haifar da da mai ido ba.Sun san da cewar sune makaranta ta biyu wajen samar da ilimi da tarbiyya bayan ta farko da Iyaye suka kasance Malamanta.
Iyaye sune makaranta ta farko wadanda da suke kasancewa wani babban ginshikin rayuwa gaba daya da su ‘ya’yansu wadanda su ne daliban, matsawar sun basu tarbiya ta gari a matsayinsu na makaranta ta farko wadda daga wurinsu ne za a fara dorasu kan tafarki nagari. Malaman makaranta ba za su fuskanci wata matsala mai yawa da har su daliban sun samu kyakkyawar tarbiya daga makaranta ta farko da Iyaye suka kasance Malamai.
Shugabannin al’umma wadannan sun hada da masu gari kamar Mai unguwa,Dagaci, Hakimi, ko Sarki da sauran manyan gari da suke da ruwa da zaki wajen ganin lalle makaranta tana tafiya kamar yadda duk makaranta yakamata. Suna yin haka ne wajen bada gudunmawa musamman ma wajen ganin makarantar bata fuskantar wata matsala da zata kawozama mata wani tarnaki wajen makarantar ta rika tafiya kafada- kafada kamar yadda sauran makarantu suke tafiyar da harkokinsu.
Kungiyar Iyaye da Malamai ba karamar gudunmawa kungiyar take badawa a makaranta ba wajen maganin duk wata matsala da ta yaso saboda sanin kowa ne,bayan ‘yanmakaranta sun baro gida zuwa makaranta har zuwa lokacin tashinsu suna tare ne da Malamai wadanda su suka san yadda suke fahimta ko gane ilimin da suke koya masu ta darussa daban-daban.Su suka fi kowa sanin irin kwazon yaran don haka sune suka fi kowa dacewa sanin kwazonsu a aji da irin halayensu.
Masu ruwa da tsaki su wadannan sun kasance ne dukwani abin da yake da nasaba da ilimi suna bayar da gudunmawa ne wannan kuma ba sai a garin da suke zama bane har ma wadanda ba garuruwan su bane na asali suna bada gudunmawa musamman ma ta bangaren ilimi domin sun san babban shine babban ginshiki na rayuwar al’umma ci gabansu.